Wannan shafin mallakarNe 2025-04-11MUNAFUKAI BA SAHABBAI BANE
GABATARWA
أن الحمد لله تعالى نحمده ونستعين به ونستغفره، ونعوذ بالله تعالى من شرور أنفسنا وسيئات أعمالنا، من يهد الله تعالى فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له، وأشهد أن لا إله إلا الله وحده لا شريك له، وأشهد أن محمدًا عبده ورسوله، أما بعد: فإن أصدف الحديث كتاب الله تعالى ، وأحسن الهدي هدي محمد صلى الله عليه وآله وسلم، وشر الأمور محدثاتهما، وكل محدثة بدعة، وكل بدعة ضلالة، وكل ضلالة في النار.
اللهم صل على محمد وعلى آل محمد كما صليت على إبراهيم وعلى آل إبراهيم في العالمين إنك حميد مجيد، وبارك على محمد وعلى آل محمد كما باركت على إبراهيم وعلى آل إبراهيم
في العالمين إنك حميد مجيد.
Bayan haka; nazabi nayi rubutu ne akan wannan mas'alar domin shubuhar da ake kawowa al'ummar annabi.
Yawanci idan mu ahlussunnah mukayi rubutu gameda ayoyinda suke magana akan falalar sahabbban manzon Allah SAW gaba dayansu, sai kaji masu wata batacciyar aqida suna cewa ai ba dukkan sahabbai ake nufi ba. tunda ai munafikai suna ciki, harma wasu suce maka yawancin sahabban duk munafikai ne. wal'iyazubillah.
Hakan yasaba da aqida ingantacciya ta ahlussunnah walja'ama.
Shiyasa nayi nufin fito wa na barrantarda sahabbai daga cikin wadancan batattun (munafukai). Duk dayake nasan akwai malamai dasuka tabayin maganganu gameda wannan mas'alar, to amma nima zanyi nawa domin idan nayi kuskure sai malamaina da abokanai n su gyara min, kunga ahaka ahaka wataran nima sai nazama malami. Ina fata Allah yamin muwafaqa a cikin rubutuna kuma yasa nayi domin shi ba domin na birge ba.
SASHI NA FARKO
Wanene sahabi?
Kalmar sahabi kalma ce ta larabci wadda asalinta shine 'sahib'
Ma'anarta biyu ce, akwai ta yare akwai ta malaman shari'ah, Toh dayake rubutuna yana da alaqa ne da shari'a zan maida hankali ne kadai akan abnd yashafi shari'ah.
Idan akace wannan sahabin annabi ne to ana nufin abinda zan kawo yanzu.
أن الصحابي هو من لقي النبي صلى الله عليه وآله وسلم في حياته مؤمناً به ومات على الإسلام
Ma'ana: hakika sahabi shine wanda yataba gamuwa da annabi, sannan suka shiga musulunci a lokacin rayuwarsa, sannan kuma suka mutu a cikin musulunci.
Kaga kenan fadin cewa wanda ya taba gamuwa da annabi hakan yashigar da makafi aciki.
Fadin cewa wanda ya musulunta alokacin rayuwar annabi yafitar da wanda ya musulunta bayan wafatin manzon Allah SAW.
Fadin cewa wanda ya mutu a musulunci ya fitarda wanda yayi ridda kafin ya mutu.
kaga kenan sai mutum ya cika wadannan sharudda kafin yasmi matsayi da kirarin sahabi.
SASHI NA BIYU
Suwanene munafukai???
munafukai sune wadanda suke boye kafurci kuma suke bayyana musulunci.
fadin cewa suna boye kafirci yana nufin cewa kafiran ne.
fadin cewa suna bayyana musulunci yana nuna cewa karya sukeyi ba musulman bane.
wani zaice menene dalilin fadin haka?
sai ince nafadi hakan ne bisa karkashin fadin ubangiji acikin suratu baqara.
Allah yace:
وَمِنَ النَّاسِ مَنْ يَقُولُ آمَنَّا بِاللَّهِ وَبِالْيَوْمِ الْآخِرِ وَمَا هُمْ بِمُؤْمِنِينَ
ma'ana: alah yace daga cikin mutane akwai wadanda suke cewa sunyi imani da allah da ranar lahira, amma su din ba masu imani bane.
sannan awata ayar allah yace:
وَإِذَا لَقُوا الَّذِينَ آمَنُوا قَالُوا آمَنَّا وَإِذَا خَلَوْا إِلَى شَيَاطِينِهِمْ قَالُوا إِنَّا مَعَكُمْ إِنَّمَا نَحْنُ مُسْتَهْزِئُونَ
ma'ana: allah yace (su wadannan mutanen) idan suka gamuda wadanda sukayi imani sai suce ai suma sunyi imani, idan kuma suka koma wajen shaidanunsu sai suce ai muma muna tare daku, ai kawai munayiwa wadancan izgili ne.
idan ka kula zakaga da allah yazo kan masu imani ai bai jinginasu da munafikai ba, amma dayazo kan shaidanun sai ya jinginasu da munafukan.
sannan awata ayar allah yace:
إِذَا جَاءَكَ الْمُنَافِقُونَ قَالُوا نَشْهَدُ إِنَّكَ لَرَسُولُ اللَّهِ وَاللَّهُ يَعْلَمُ إِنَّكَ لَرَسُولُهُ وَاللَّهُ يَشْهَدُ إِنَّ الْمُنَافِقِينَ لَكَاذِبُونَ
ma'ana: allah yace: idan munafukai sukazo maka suna cemaka suna cewa sun shaida kai manzon allah ne, ai dama allah yasan kai manzonsa ne, sannan kuma allah yana shaidawa cewa munafukai karya sukeyi (basu yarda kai manzon allah bane).
idan muka dubi sakamakon da wadannan ayoyi suke bamu zamuga cewa su munafikai kawai suna fadan musulunci ne abaki amma sam-sam babu shi acikin zuciyoyinsu.
wani zai iya cewa ai sun hada ne tsakanin musuluncin da kafircin.
sai muce masa ai ba'a hada musulunci da kowane addini. idan kuwa mutum yahada musulunci da wani addini to kawai yazama dan wancan addinin kuma baya cikin musulunci.
allah yace:
وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الْآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ
ma'ana: duk wanda yanemi wani addini wanda ba musulunci ba to baza'a amsa daga gareshi ba, kuma a ranar lahira yana cikin tababbu.
SASHI NA UKU
menene yahana munafukai shiga jerin sahabbai?
ian baka manta ba abaya mun kawo maka sharuddan da mutun zai cika kafi yazama sahabi. sannan kuma kaamar yadda muka fada shsruddan guda uku ne.
idan har jka tuna wannan kuma kahada da ma'anar da aka bayar gameda munafukai zaka gano cewa ba sahabbai bane.
kankawo abin a rarrabe domin a fahimce shi dalla dalla.
kamar yadda aka fada cewa sharadi na farko na zama sahabi shine gamuwa da annabi.
ko shakka babu cewa munafukai sun cika wannan sharadin na farko saboda sun rayu lokaci daya da annabi.
to sun cika sharadi daya saura biyu.
sannan sharadi na biyu shine dole yazamanto mutum musulmi ne lokacinda yagamuda annabin. to a karkashin wannan maganar zamuga babu su aciki , saboda su ai basuyi imanin ba. ayoyi da yawa sun nuna cewa munafukai kafirai ne ba musulmi ba. kaga kuwa babu tayadda za'ayi kafiri yazama sahabin annabi indai a ma'anarta ta shari'ah ne. amma in a ma'anar yare ne wannan zasu iya zama. mukuwa muna magana ne akan shari'ah ba yare ba. domin annabinmu ba yare yazo koya mana ba, shari'ah yazo koya mana.
wani zaice menene dalili akan cewa munafukai kafirai ne?
kaduba ayoyin da nakawo abaya dakuma wadanda amkawo anan gaba kadan inshaallah, idan kahadasu zaka gano cewa kafirai ne. ga ayoyin kkamar haka:-
allah yace:
وَمَا مَنَعَهُمْ أَنْ تُقْبَلَ مِنْهُمْ نَفَقَاتُهُمْ إِلَّا أَنَّهُمْ كَفَرُوا بِاللَّهِ وَبِرَسُولِهِ وَلَا يَأْتُونَ الصَّلَاةَ إِلَّا وَهُمْ كُسَالَى وَلَا يُنْفِقُونَ إِلَّا وَهُمْ كَارِهُونَ
ma'ana: allah yace: babu abinda yahana a amshi sadakarsu sai don kawai sun kafircewa allah da manzonsa, sannan basu zuwa sannan sai a kasalance (ba ason ransu ba) sannan basu bada sadaka sai ransu yana ki.
wannan ayar tanuna cewa kafirai ne, dama ai si arne duk ainda zaiyi koda mai kyau ne to bashi da lada awajen allah
awata ayar kuma allah yace:-
وَلَا تُصَلِّ عَلَى أَحَدٍ مِنْهُمْ مَاتَ أَبَدًا وَلَا تَقُمْ عَلَى قَبْرِهِ إِنَّهُمْ كَفَرُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ وَمَاتُوا وَهُمْ فَاسِقُونَ
ma'ana: daga yanzu kadena yin sallah(ta gawa) akan duk wanda yamutu daga cikinsu (munafukai) kuma kadena tsayawa kana addu'ah akan qabarinsu. hakika su sun kafircewa allah kuma sun mutu suna fasikai.
itama wannar ayar takara nuna mana cewa kafirai ne.
awata ayar daban kuma allah yace:
وَلَا تُعْجِبْكَ أَمْوَالُهُمْ وَأَوْلَادُهُمْ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ أَنْ يُعَذِّبَهُمْ بِهَا فِي الدُّنْيَا وَتَزْهَقَ أَنْفُسُهُمْ وَهُمْ كَافِرُونَ
ma'ana: allah yacewa annabi; kada dukiyoyinsu da yayayensu su baka mamaki ko su birgeka, allah yanaso ya azabtar dasu ne dasu a duniya kuma ransu yana fita ne alhalin suna kafirai (kamar yadda ibn abbas yafassara)
sannan allah yace:-
يَحْذَرُ الْمُنَافِقُونَ أَنْ تُنَزَّلَ عَلَيْهِمْ سُورَةٌ تُنَبِّئُهُمْ بِمَا فِي قُلُوبِهِمْ قُلِ اسْتَهْزِئُوا إِنَّ اللَّهَ مُخْرِجٌ مَا تَحْذَرُونَ
ma'ana: munafukai suna tsoron kada asaukarda ayarda zata bayyana abinda yake cikin zuciyoyinsu. yakai annabi kace musu sucigaba da yin izgili watarn allah zai baiyana abinda suke tsoro.
sannan allah yace:-
وَأَمَّا الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمْ مَرَضٌ فَزَادَتْهُمْ رِجْسًا إِلَى رِجْسِهِمْ وَمَاتُوا وَهُمْ كَافِرُون
ma'ana:ammasu wadanda suke da rashin lafiya a zuciyarsu (munafukai) idann aya gtasauka sai takara musu datti akan dattinda zuciyarsu take dashi kuma sun mutu suna kafirai.
allah yace:-
يَحْلِفُونَ بِاللَّهِ مَا قَالُوا وَلَقَدْ قَالُوا كَلِمَةَ الْكُفْرِ وَكَفَرُوا بَعْدَ إِسْلَامِهِمْ وَهَمُّوا بِمَا لَمْ يَنَالُوا
ma'ana(wata rana wani munafuki yana gida tareda dansa sai yafadi munnunar magana gameda anabi, sa yaron yaje yafadawa annabi, da aka kirawo mutumin domin kare kansa sai ya rantse akan bai fada ba), sai allah yasaukarda aya yace: munafunafukai suna rantsuwa wai basu fadi abinda akace sun fada ba. amma karya ne hakika sun fadi kalmar kafirci (domin yiwa allah da manzonsa izgili kafirci ne) kuma sun kafirta bayan imaninsu. kuma hakika suna burin abinda bazasu samuna (na kyakkyawan rabo a lahira). amma kamar yadda ya tabbata cewa mutumin ya musulunta daga baya.
sannan allah yace:
اسْتَغْفِرْ لَهُمْ أَوْ لَا تَسْتَغْفِرْ لَهُمْ إِنْ تَسْتَغْفِرْ لَهُمْ سَبْعِينَ مَرَّةً فَلَنْ يَغْفِرَ اللَّهُ لَهُمْ ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ كَفَرُوا
بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ وَاللَّهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ
ma'ana: allah yana gayawa manzonsa yace: ko kanema musu gafara ko karka nema musu gafara, koda zaka nema musu gafara sau saba'in allah bazai gafarta musu ba. hakan kuwa zai farune saboda sun kafircewa allah da manzonsa.
ayoyin suna da yawa amma anan zan tsaya da kawo su.
idan baka manta ba muna magana ne acikin sharadi ba biyu na zama sahabi.
kaga kenan koda sun cika sharadi na farko to basu cika na biyu ba.
ammafa idan munafiki yatuba a lokacin annabi kuma har ya mutu acikin musulunci to yazama sahabi.
saikuma sharadi na uku.
sharadi na uku shine dole sai mutum yamutiu a musulunci.
ayoyinda nakawo abaya kuwa sun tabbatar mana da cewa munafukai basu mutu a musulunci ba.
sannan koda mutum yagamuda annabi kuma yayi imani dashi a lokacin rayuwarsa amma kuma sai yai ridda kuma har ya mutu ahaka to ba sahabi bane, idan kuma yatuba bayan riddar kuma yariga yacika wadancan sharudan guda biyu to sahabi ne.
anan zan takaita wannan rubutun nawa. fatana shine allah yasa sakon ya isa inda ake bukata.
kamar kullum ina nan ina jiran gyara, tambaya ko shawara gameda wannan rubutun dama sauran rubututtuka na.
wassalamu alaikum warahmatullah.
AWAISU HARUNA MUHAMMAD
AL'ARABEE FAGGE BA'A GANIN ALLAH A DUNIYA
Gabatarwa
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستهديه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا ومن سيئات أعمالنا من يهده الله فلا مضل له ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن لا إله إلا الله وحده لا شريك له ، وأشهد أن محمد عبده ورسوله : ( يَا أَيُّهَا النَّاسُ اتَّقُوا رَبَّكُمْ الذِي خَلقَكُمْ مِنْ نَفْسٍ وَاحِدَةٍ وَخَلقَ مِنْهَا زَوْجَها وَبَثَّ مِنْهُمَا رِجَالا كَثِيرًا وَنِسَاءً وَاتَّقُوا اللهَ الذِي تَتَساءَلُونَ بِهِ وَالأَرْحَامَ إِنَّ اللهَ كَانَ عَليْكُمْ رَقِيبًا ) ، أما بعد فإن خير الحديث كتاب الله وخير الهدي هدي محمد صلى الله عليه وسلم وشر الأمور محدثاتها وكل محدثة بدعة وكل بدعة ضلالة وكل ضلالة في النار .
Bayan haka; ina yiwa yan uwana musulmi sallama irin ta addinin musulunci Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.
Wannan rubutun zai maida hankaline ga rushe wata akida da tadade tana kewayawa tsakanin al'ummar musulmi.
Al'ummar musulmi tana fama da matsaloli dayawa wanda kuma yakamata ace tadade dayin maganinsu, amma har yanzu abin yaci tura.
Daga cikin matsalolin da muke fama dasu shine 'Rashin kwararru kuma gogaggun malamai masu karantar da addinin Allah'. Hakan ne yasa kowa kawai daya kulle kansa a daki yakaranta wasu yan littattafai wadanda basu taka kara sun karya ba sai yafito yanada rawani yasamo sanda wai shima yazama malami.
Dama ai annabi yafada yace yana daga cikin alamomin tashin alkiyama faruwar hakan. Ga hadisin da yanuna haka:-
حَدَّثَنَا مُسَدَّدٌ قَالَ حَدَّثَنَا يَحْيَى عَنْ شُعْبَةَ عَنْ قَتَادَةَ عَنْ أَنَسِ قَالَ لَأُحَدِّثَنَّكُمْ حَدِيثًا لَا يُحَدِّثُكُمْ أَحَدٌ بَعْدِي سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ مِنْ أَشْرَاطِ السَّاعَةِ أَنْ يَقِلَّ الْعِلْمُ وَيَظْهَرَ الْجَهْلُ وَيَظْهَرَ الزِّنَا وَتَكْثُرَ النِّسَاءُ وَيَقِلَّ الرِّجَالُ حَتَّى يَكُونَ لِخَمْسِينَ امْرَأَةً الْقَيِّمُ الْوَاحِدُ
Ma'ana: annabi yace yana daga cikin alamun tashin kiyama za'a samu karancin ilimi, kuma jahilci zai baiyana, sannan zina zata yawaita, sannan mata zasuyi yawa, har sai yakasance namiji dayane zai kasance tsayayye akan mata hamsin.
(bukhariy 81)
Fadin annabi nacewa za'a sami karancin ilimi, bawai yana nufi kowa zai wayi gari bane yaji yazama jahili. Allah zai dauke ilimi ne ta hanyar kashe malamai kamar yadda haidisi ya tabbata.
حدثنا بكر قال نا عمرو قال نا عبد العزيز بن الحصين عن هشام بن عروة عن أبيه عن عبد الله بن عمرو قال قال رسول الله صلى الله عليه و سلم إن الله عز و جل لا يقبض العلم انتزاعا ينتزعه من الناس ولكن يقبضه بقبض العلماء حتى إذا لم يزل عالما ااتخذ الناس رءوسا جهالا فسئلوا فأفتوا بغير علم فضلوا وأضلوا
Ma'ana: annabi sallalllahu alaihiwasallam yace "hakika Allah ba dauke ilimi dauke ilimi zaiyi ba tahanyar tsame shi daga cikin al'umma, sai de zai dauke shi ne ta hanyar dauke malamai (mutuwarsu). Har sai an wayi gari babu balamai, sai mutane su riki wasu jahilai amatsayin malamai, sai adinga tambayarsu sukuma suna bayarda fatawa bada ilimi ba, sai su bata kuma su batar".
(mu'ujamul awsad 3222)
Toh wannan abinda sadiqul masduqu yafada yau gashi munaganinsa da idonmu.
Sai kuma abu na biyu shine; yayinda malami yamutu akasar hausa toh bawai ana dubawa bane aga waye ya cancanta yagaji kujerar malamin. Kawai za'a dauko dansa ne asaka shi awajen koda ya cancanta ko bai cancanta ba. hakan ne yasa idan uba malami yayi wani kuskure toh yayinda dansa yagaje shi, toh ko yasan abinda uban yayi kuskure ne ba lallle ya iya dukan kirji yafito yace ba dede bane. Saide kawai ayi rufa-rufa atafi ahaka.
Amma da ace ana dauko wanda ya canacnata ya karantar da al'umma to in wancan kuskure yayi bazai ji kunyar gyarawa ba tunda ba mahaifinsa bane.
Mas'alarda nakeson yin magana akan ta itace mas'alar GANIN ALLAH A DUNIYA DAKUMA LAHIRA.
Ansamu banbancin malamai na yanzu dana da akan cewa shin akwai yiwuwar ganin Allah a duniya ko babu.
Zan dauki mas'alar nayi bayaninta iyakar abinda Allah yahore min na ilimi bisa dogaro da ayoyin Allah da hadisan manzon Allah sallalllahu alaihi wasallam. Ina rokon Allah yamin muwafaqa wajen rubuta dai-dai kuma idan nayi daidai din ya amsa sannan yasa sakon ya isa gun wadanda akayi domin su.
SASHI NA FARKO
BA'A GANIN ALLAH A DUNIYA
Kamar yadda dalilai dayawa suka tabbata cewa idanun mutum ko aljani ko mala'ika ko wata halitta tadaban bazasu iya daukar nauyin ganin ubangiji ba.
Samfirin halittar da Allah yayi mana bana ganinshi bane ahalin yanzu.
Ayar da zan fara kawowa a wannan bangaren itace wadda ake bamu labarin munajatin da Allah yayi dashi da annabi Musa alaihissalam. Allah yace
وَلَم?َّا جَاءَ مُوسَى لِمِيقَاتِنَا وَكَلَّمَهُ رَبُّهُ قَالَ رَبِّ أَرِنِي أَنْظُرْ إِلَيْكَ قَالَ لَنْ تَرَانِي وَلَكِنِ انْظُرْ إِلَى الْجَبَلِ فَإِنِ اسْتَقَرَّ مَكَانَهُ فَسَوْفَ تَرَانِي فَلَمَّا تَجَلَّى رَبُّهُ لِلْجَبَلِ جَعَلَهُ دَكًّا وَخَرَّ مُوسَى صَعِقًا فَلَمَّا أَفَاقَ قَالَ سُبْحَانَكَ تُبْتُ إِلَيْكَ وَأَنَا أَوَّلُ الْمُؤْمِنِينَ
Ma'ana: yayinda Musa yazo wajenda muka umarce shi (madyana) kuma ubangijinsa yayi magana dashi sai annabi musa yace ya ubangiji inaso kabari inganka, sai Allah yace masa bazaka ganni ba (a duniya), toh amma kalli wancan dutsen, zan saukar da kadan daga cikin haskena idan har dutsen ya iya daukar ganina to kaima zakaganni. Yayinda Allah yasaukarda haskensa akan dutsen sai dutsen ya tarwatse. Shikuma annabi Musa sai yafadi yasuma, yayinda ya farfado sai yace tsarki ta yabbata gareka ya ubangiji, natuba izuwa gareka, kuma nine farkon muminai (acikin al'umma ta).
Ga wadanda sukasan harshen larabci sunsan cewa kalmar 'لن' tana kore abu ne amma ba dindindin ba, aa zuwa wani dan lokaci. Kenan ayar tanuna cewa annabi musa duk da matayin annabta dayake dashi amma bazai sami damar ganin Allah ba a duniya sai de in anje lahira.
Awata ayar kuma Allah yace:-
لَا تُدْرِكُهُ الْأَبْصَارُ وَهُوَ يُدْرِكُ الْأَبْصَارَ وَهُوَ اللَّطِيفُ الْخَبِيرُ
Zan dauko fassarar da Abdullahi bn abbas yayi wa ayar don karma kace mune kuma fassara
Ibn Abbas yace:-
{ لاَّ تُدْرِكُهُ الأبصار } في الدنيا ولا يرى الخلق ما يرى هو وتنقطع دونه الأبصار بالكيفية في الآخرة وبالرؤية في الدنيا
Ma'ana: gani baya riskarsa (Allah) aduniya, sannan halittunsa basa ganin abinda yake gani…….
Kaga kenan munsami tabbacin cewa ba'a ganin Allah a duniya.
SASHI NA BIYU
ZA'AGA ALLAH A LAHIRA
Tunda ankore ganin mahaliccinmu a duniya amma ansamu garabasar ganin Allah a aljanna (ga muminai kadai).
Kasani cewa ganin Allah abu ne maidadin gaske kuma abune mai girman da yafi komai dadi da saka farin ciki a rayuwar dan adam.
Allah dakansa yatabbatar mana da cewa muminai zasu ganshi a aljannah.
Allah yace وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَاضِرَةٌ (*) إِلَى رَبِّهَا نَاظِرَ
Ma'ana: wadansu fuskoki awannan ranar(kiyama) suna cike da ni'ima da annashuwa, kuma zasuga ubangijinsu.
Wannan ayar ta tabbatar mana da cewa muminai zasuga Allah a lahira.
Hadisai da dama sun tabbatar mana cewa muminai zasuga ubangijinsu amma a lahira ba a duniya ba. misali:-
حَدَّثَنَا إِسْحَاقُ بْنُ إِبْرَاهِيمَ عَنْ جَرِيرٍ عَنْ إِسْمَاعِيلَ عَنْ قَيْسِ بْنِ أَبِي حَازِمٍ عَنْ جَرِيرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ قَالَ كُنَّا جُلُوسًا لَيْلَةً مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَنَظَرَ إِلَى الْقَمَرِ لَيْلَةَ أَرْبَعَ عَشْرَةَ فَقَالَ
إِنَّكُمْ سَتَرَوْنَ رَبَّكُمْ كَمَا تَرَوْنَ هَذَا لَا تُضَامُونَ فِي رُؤْيَتِهِ
Ma'ana: jarir bin Abdullah yace watarana muna kasance tareda manzon Allah sallallahu alaihi wasallam, sai yayi duba izuwa wata alhalin yana daren goma sha hudu, sai yace hakika zakuga ubangijinku (a lahira) kamar yadda kuke ganin wannan watan bakuyin rige-rige wajen ganinsa.
Akwai wani hadisiwanda shima yana nuna mana karara cewa yan aljanna zasuga Allah acikin aljannah. Ga hadisin kamar haka:-
حدثنا أحمد بن بشير الطيالسي قال حدثنا هدبة بن خالد قال حدثنا حماد بن سلمة عن ثابت البناني عن عبد الرحمن بن أبي ليلى عن صهيب أن رسول الله قال : في هذه الآية { للذين أحسنوا الحسنى وزيادة } قال إذا دخل أهل الجنة الجنة وأهل النار النار نادى مناد يا أهل الجنة إن لكم عند الله موعدا يريد أن ينجزكموه فيقولون وما هو ألم يبيض وجوهنا ألم يثقل موازيننا ألم يزحزحنا عن النار ويدخلنا الجنة فيكشف لهم عن الحجاب فينظرون إلى الله عز و جل فما شيء أحب إليهم من النظر إليه
Ma'ana: hakika annabi sallallahu alaihi wasallam yace gameda ayar (للذين أحسنوا الحسنى وزيادة) yace: idan yan aljanna suka shiga aljanna kuma yan wuta suka shiga wuta sai wani mai kira yayi kira ga yan aljannah, sai yace akwai wani alkawari tsakaninku da ubangijinku wanda yayi muku kuma ba'a cika muku shiba sai yansu yakeso yacika muku. Sai suce; ba Allah ya haskaka fuskokin mu ba? ba Allah ya nauyaya mizaninmu ba? ba Allah ya tseratar damu daga wuta ba? ba Allah yashigar damu aljannah ba? toh kuma meye yayi saura? Sai ayaye hijabi sai suga ubangijinsu. Sai suji aransu ba abinda sukafi so fiyeda ganin ubangijin nasu.
(mu'ujamul awsad 756)
Wannan hadisin ya tabbatar mana da cewa ana ganin Allah amma a aljannah. Banda a duniya kuma banda yan wuta.
SASHI NA UKU
ANNABI YAGA ALLAH KO BAI GANI BA?
Wannan itace gabarda nayi rubutuna saboda ita, toh amma dama yakamata duk wanda zaiyi wannan maganar yayi doguwar shimfida kafin yazo kanta saboda za'afi fahimtar bayaninsa.
Wasu malamai dayawa suna cewa wai annabi yaga Allah, mukuwa bisa ga dalilai dasuka bayyana garemu mun tabbatar cewa manzon tsira kuma cikamakin annabawa baiga Allah ido da ido ba saidai muna da tabbacin yaganshi a mafarki.
Hadisin da annabi yafada yace yaga Allah a mafarki shine:-
حَدَّثنا مُحَمد بن المثنى ، قال : حَدَّثنا معاذ بن هشام قال حدثني أبي عن قتادة ، عَن أبي قلابة عن خالد بن اللجلاج عن عَبد الله بن عباس ، رَضِي الله عنهما ، أن نبي الله صلى الله عليه وسلم قال : رأيت ربي في أحسن صورة فقال : يا محمد فقلت : لبيك ربي وسعديك قال : فيم
يختصم الملأ الأعلى ؟ قلت : ربي لا أدري................ .
Ma'ana: hakika naga ubangijina (a mafarki) acikin mafi kyawun sura, sai yace min: ya Muhammad, sai nace amsa kiranka ya ubangijina, sai yace wai akan me mala'iku suke ta rige-rige? Sai nace ban sani ba ya Allah…………
(kutubus-sitta da asaniyn).
Wannan hadisin ya tabbatar mana da cewa annabi yana ganin Allah amma a mafarki. Wadanda suke cewa annabi yana Allah idan ka tambayesu zakaga basu dawasu kwararan dalilai dasuke nuna hakan sai de suyi ta misalce misalce.
Akwai wata aya da take da wani abin mamaki. Da ita wasu suke kafa hujja wajen cewa annabi yaga Allah, sannan tana daga cikin dalilanmu akan cewa annabi bai ga annabi ba Allah. Wannan ayar itace:-
عَلَّمَهُ شَدِيدُ الْقُوَى (5) ذُو مِرَّةٍ فَاسْتَوَى (6) وَهُوَ بِالْأُفُقِ الْأَعْلَى (7) ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّى (8) فَكَانَ قَابَ قَوْسَيْنِ أَوْ أَدْنَى (9) فَأَوْحَى إِلَى عَبْدِهِ مَا أَوْحَى (10) مَا كَذَبَ الْفُؤَادُ مَا رَأَى (11) أَفَتُمَارُونَهُ عَلَى مَا يَرَى (12) وَلَقَدْ رَآهُ نَزْلَةً أُخْرَى (13) عِنْدَ سِدْرَةِ الْمُنْتَهَى
Dayake masu cewa annabi yaga Allah suna kafa hujjah ne da wani hadisin abdullahi ibn Abbas, zan kawo fassarar wannan ayar ne daga cikin tafsirin ibn Abbas din. Dama ai banda annabi babu wanda yakaishi ilimin tafsirin alqur'ani mai girma.
Ga abinda ibn Abbas yake cewa;-
{ ذُو مِرَّةٍ فاستوى } جبريل في صورته التي خلقه الله عليها ويقال فاستوى في صورة خلق حسن { وَهُوَ بالأفق الأعلى } بمطلع الشمس ويقال في السماء السابعة { ثُمَّ دَنَا } جبريل إلى محمد صلى الله عليه وسلم . ويقال محمد إلى ربه { فتدلى } فتقرب { فَكَانَ قَابَ قَوْسَيْنِ } من قسي العرب { أَوْ أدنى } بل أدنى بنصف قوس { فأوحى إلى عَبْدِهِ } جبريل { مَآ أوحى } إلى عبده محمد عليه السلام ويقال فأوحى جبريل إلى عبده محمد عليه السلام ما أوحى الذي أوحى ويقال فأوحى إلى عبده محمد الذي أوحى { مَا كَذَبَ الفؤاد } فؤاد محمد صلى الله عليه وسلم { مَا رأى } الذي رأى ربه بقلبه ويقال رأى ربه بفؤاده ويقال ببصره وهذا جواب القسم فلما أخبرهم النبي عليه السلام كذبوه فنزل { أَفَتُمَارُونَهُ } أفتكذبونه { على مَا يرى } على ما قدر أي محمد عليه السلام وإن قرأت بالألف يقول أفتجادلونه على ما قد رأى { وَلَقَدْ رَآهُ } يعني رأى محمد عليه السلام جبريل ويقال ربه بفؤاده ويقال ببصره { نَزْلَةً أخرى } مرة أخرى غير التي أخبركم بها { عِندَ سِدْرَةِ المنتهى } التي ينتهي إليها كل ملك مقرب ونبي مرسل ويقال ينتهي إليها علم كل ملك مقرب ونبي مرسل وعالم راسخ
Ma'ana: Abdullahi bin Abbas yace: (ذُو مِرَّةٍ فاستوى) ai jibrilu ne yadaidaita bisa ga kyakkyawar halittarsa da Allah yai masa.
(وَهُوَ بالأفق الأعلى) sama ta bakwai kenan ko kuma mahudar rana.
(ثُمَّ دَنَا) sai jibrilu yamatso zuwaga annabi (فتدلى) sai yakara matsowa. (فَكَانَ قَابَ قَوْسَيْنِ) saida suka zamanto kamar bakin baka guda biyu (أَوْ أدنى) kokuma rabinsu. (فأوحى إلى عَبْدِهِ) sai Allah yayi wahayi ga bawansa jibrilu (مَآ أوحى) abinda (jibrilu)yayi wahayinsa ga annabi Muhammadu sallallahu alaihi wasallam
(مَا كَذَبَ الفؤاد) tunanin annabi Muhammad baiyi karya ba akan
(مَا رأى) abinda yagani a lokacinda yaga ubangijinsa da zuciyarsa, wasu kuma sukace da tunaninsa wasu kuma sukace da idonsa. (أَفَتُمَارُونَهُ) yaku kafirai kuna jayayya da annabi ne (على مَا يرى) akan abinda yace muku yagani? (وَلَقَدْ رَآهُ) hakika annabi yaga jibrilu, wasu kuma sukace yaga annabi da idanunsa (نَزْلَةً أخرى) awani lokacin daban da wanda yagaya muku, (عِندَ سِدْرَةِ المنتهى) yaganshi ne a magaryar tikewa wadda itace karshen wajenda wani makusancin mala'ika da makusantan manzanni suke iya zuwa. (amma shi annabi ya wuce ta yakara gaba kamar yadda ya tabbata a hadisin isra'i da mi'iraji).
Allahu akbar! Wannan itace fassarar ibn Abbas gameda wannan ayoyin. Kuma indai gaskiya kakeso zaka fahimci cewa yafassara ayoyin akan cewa annabi baiga Allah a idanunsa ba amma yaganshi da zuciyarsa/tunaninsa.
Wani zai iya cewa ai ibn Abbas yakawo maganar masu cewa annabi yaga Allah da idanunsa. To ai a ka'idar malaman tafsiri, idam mai tafsiri yakawo fassarori dayawa to wadda yafara kawowa itace matabbaciya awajensa. Kaga genan idan mukabi wannan ka'idar zamuga cewa a ra'ayinsa annabi yaga Allah ne da zuciyarsa.
Fadin cewa 'hakika yaganshi awani lokacin na daban, a sirdatul muntaha' yana kara nuna mana cewa annabi jibrilu yagani ba Allah ba. hakan yatabbata a hadisi ingantacce da zan kawo;
حدثنا محمد بن عبد الله الحضرمي ثنا جمهور بن منصور ثنا إسماعيل بن مجالد عن مجالد عن الشعبي عن ابن عباس : أنه كان يقول في قوله { ولقد رآه بالأفق المبين } إنما أعنى جبريل عليه السلام أن محمدا صلى الله عليه و سلم رآه في صورة عند سدرة المنتهى
Ma'ana: abdullahi bn Abbas yace gameda wannan ayar, yace annabi yaga jibrilu ne a sidratul muntaha.
(mu'ujamul kabir 12565)
Awani hadisin irin wannan amma mai banbancin riwaya shikuma cewa akayi;
خبرنا أحمد بن علي بن المثنى حدثنا القواريري حدثنا يحيى بن سعيد القطان حدثنا حماد بن سلمة حدثنا عاصم عن زر عن عبد الله قال : قال رسول الله صلى الله عليه و سلم : ( رأيت جبريل عند سدرة المنتهى وعليه ست مئة جناح
Ma'ana: annabi yace naga jibrilu a sidratil muntaha, yanada fikafikai guda dari shida.
(sahih ibn hibban 6428, abi ya'ala 5360,musnad ahmad 3915,4369)
Awani bangaren daban kuma akwai wadansu hadisai dazasu taimaka mana domin kara fahimtar wannan mas'alar. Misali;
حَدَّثَنَا أَبُو بَكْرِ بْنُ أَبِى شَيْبَةَ حَدَّثَنَا وَكِيعٌ عَنْ يَزِيدَ بْنِ إِبْرَاهِيمَ عَنْ قَتَادَةَ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ شَقِيقٍ
عَنْ أَبِى ذَرٍّ قَالَ سَأَلْتُ رَسُولَ اللَّهِ -صلى الله عليه وسلم- هَلْ رَأَيْتَ رَبَّكَ قَالَ « نُورٌ أَنَّى أَرَاهُ ».
Ma'ana: abi zar yatambayi annabi yace: yasarusullah shin kaga ubangijinka? Sai annabi yace ai haske nagani, tayaya za,ayi naganshi?
(muslim 461)
Allahu akbar! Kunji dai daga bakin annabi cewa hasken ubangiji yagani ba ubangijin ba.
Awani hadisin kuma akace:-
حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ بَشَّارٍ حَدَّثَنَا مُعَاذُ بْنُ هِشَامٍ حَدَّثَنَا أَبِى ح وَحَدَّثَنِى حَجَّاجُ بْنُ الشَّاعِرِ حَدَّثَنَا عَفَّانُ بْنُ مُسْلِمٍ حَدَّثَنَا هَمَّامٌ كِلاَهُمَا عَنْ قَتَادَةَ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ شَقِيقٍ قَالَ قُلْتُ لأَبِى ذَرٍّ لَوْ رَأَيْتُ رَسُولَ اللَّهِ -صلى الله عليه وسلم- لَسَأَلْتُهُ فَقَالَ عَنْ أَىِّ شَىْءٍ كُنْتَ تَسْأَلُهُ قَالَ كُنْتُ أَسْأَلُهُ هَلْ رَأَيْتَ رَبَّكَ قَالَ أَبُو ذَرٍّ قَدْ سَأَلْتُ فَقَالَ « رَأَيْتُ نُورًا ».
Ma'ana: abdullahi bin shaqiq yake cewa abi zar, da ace zanga annabi dana tambaye shi, sai yace mai zaka tambayeshi? Sai yace zance masa ne shin yaga ubangijinsa? Sai abi zar yace to aini na tambaye shi sai yace min haske yagani.
(muslim 462).
Awani hadisin kuma akace:-
حَدَّثَنَا أَبُو بَكْرِ بْنُ أَبِى شَيْبَةَ حَدَّثَنَا عَلِىُّ بْنُ مُسْهِرٍ عَنْ عَبْدِ الْمَلِكِ عَنْ عَطَاءٍ عَنْ أَبِى هُرَيْرَةَ
(وَلَقَدْ رَآهُ نَزْلَةً أُخْرَى) قَالَ رَأَى جِبْرِيلَ.
Ma'ana: abu hurayra yace gameda wannan ayar, yace ai jibrilu yagani.
(muslim 453)
Awani hadisin kuma akace:-
حَدَّثَنَا أَبُو بَكْرِ بْنُ أَبِى شَيْبَةَ حَدَّثَنَا حَفْصٌ عَنْ عَبْدِ الْمَلِكِ عَنْ عَطَاءٍ عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ قَالَ رَآهُ بِقَلْبِهِ.
Ma'ana: abdullahi bin Abbas yace "annabi yaga Allah ne da zuciyarsa"
(muslim 454)
Awani hadisin kuma akace:-
حَدَّثَنَا أَبُو بَكْرِ بْنُ أَبِى شَيْبَةَ وَأَبُو سَعِيدٍ الأَشَجُّ جَمِيعًا عَنْ وَكِيعٍ - قَالَ الأَشَجُّ حَدَّثَنَا وَكِيعٌ - حَدَّثَنَا الأَعْمَشُ عَنْ زِيَادِ بْنِ الْحُصَيْنِ أَبِى جَهْمَةَ عَنْ أَبِى الْعَالِيَةِ عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ قَالَ (مَا كَذَبَ الْفُؤَادُ مَا رَأَى) (وَلَقَدْ رَآهُ نَزْلَةً أُخْرَى) قَالَ رَآهُ بِفُؤَادِهِ مَرَّتَيْنِ.
Ma'ana: Abdullahi bn Abbas yace gameda wadannan ayoyin guga biyu "yaganshi da zuciyarsa sau biyu"
(muslim 455)
وَحَدَّثَنَا ابْنُ نُمَيْرٍ حَدَّثَنَا أَبُو أُسَامَةَ حَدَّثَنَا زَكَرِيَّاءُ عَنِ ابْنِ أَشْوَعَ عَنْ عَامِرٍ عَنْ مَسْرُوقٍ قَالَ قُلْتُ لِعَائِشَةَ فَأَيْنَ قَوْلُهُ (ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّى فَكَانَ قَابَ قَوْسَيْنِ أَوْ أَدْنَى فَأَوْحَى إِلَى عَبْدِهِ مَا أَوْحَى) قَالَتْ إِنَّمَا ذَاكَ جِبْرِيلُ -صلى الله عليه وسلم- كَانَ يَأْتِيهِ فِى صُورَةِ الرِّجَالِ وَإِنَّهُ أَتَاهُ فِى هَذِهِ الْمَرَّةِ فِى صُورَتِهِ الَّتِى هِىَ صُورَتُهُ فَسَدَّ أُفُقَ السَّمَاءِ.
Ma'ana: masruq yake cewa A'isha (a lokacinda tace masa annabi baiga Allah ba) to itakuma wannan ayar fa da Allah yace 'walaqad ra'ahu', sai tace masa ai wannan jibrilu ne, annabi yagan shi a surarsa ta ainahi, da yakasance yana zuwa masa a surar mutum. Sai aranar ne yaganshi a surarsa ta ainahi a sararin samaniya.
(muslim 460)
Sannan awani hadisin akace:-
ورواه ابنُ جرير، عن ابن حُمَيد، عن مِهْرَان، عن موسى بن عبيدة، عن محمد بن كعب، عن بعض أصحاب النبي صلى الله عليه وسلم قال: قلنا: يا رسول الله، هل رأيت ربك؟ قال: "لم أره بعيني، ورأيته بفؤادي مرتين" ثم تلا { ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّى }
Ma'ana: wani sashi daga cikin sahabban annabi sukece masa, shin kaga ubangijinka? Sai annabi yace ban ganshi da idona ba amma naganshi da zauciyata.
(tafsiru dabariy, karkashin fassarar ayar)
Sannan wani hadisin kuma yace:-
حدثنا محمد بن مجاهد، حدثنا أبو عامر العقدي، أخبرنا أبو خلدة، عن أبي العالية قال: سُئِل رسول الله صلى الله عليه وسلم: هل رأيت ربك؟ قال: "رأيت نهرا، ورأيت وراء النهر حجابا، ورأيت وراء الحجاب نورا لم أر غير"
Ma'ana: antambayi annabi akace masa kaga ubangijinka? Sai yace "naga kogi sannan bayan kogin sai naga wani hijabi, sannan sai naga wani haske abayan hijabin bayan nan kuma banga komai ba".
(ibn kathir karkashi fassarar ayar)
Akwai wani hadisi da wasu zasu iya kafa hujja dashi wajen cewa ai annabi yaga Allah. Ga hadisin kamar haka;-
حدثنا الحسن بن محمد بن الصباح، حدثنا محمد بن عبد الله الأنصاري، أخبرني عَبَّاد بن منصور قال: سألت عكرمة: { مَا كَذَبَ الْفُؤَادُ مَا رَأَى } ، فقال عكرمة: تريد أن أخبرك أنه قد رآه؟ قلت: نعم. قال: قد رآه، ثم قد رآه.
Ma'ana: antambayi ikrama gameda wannan ayar sai yace "kanaso ne ince maka yaganshi"? sai mutumin yace"eh", sai ikramah yace "hakika yaganshi, hakika yaganshi, hakika yaganshi".
To ai ana nufin yaganshi ne da idanunsa. Domin kuwa ikramah dalibin ibn Abbas ne kuma fatawar ibn Abbas itace yaganshi da zuciyarsa.
Kaddarama ba haka yake nufi ba. toh yanzu idan ibn Abbas yayi fassara sannan ikramah yayi fassara dan Allah dawacce fassara zaka yarda?
Zan tsaya da kawo dalilai anan ba don sun kare ba. wallahi saide don muna da ragowar aiyuka dayawa akan wasu mas'alolin daba wannan ba.
Nasan yawancin masu aqidar cewa annabi yaga Allah da idanunsa idan munzo munyi wannan maganar suna jifanmu da cewa bama son annabi ne shiyasa muke fadin haka; wal'iyazu billah, haba dan uwa! Kadubi rubutuna sosai da idon basirah. Bankawo maganata ba amatsayina na Awaisu Haruna, bankawo maganar malamina Sheikh Anas Assalafiy Fagge ba, ban kawo maganar sheikh Jafar Mahmud Adam ba, ban kawo maganar malam Abubakar Gumi ba, maganar Nasirudden Albani ba. ban kawo maganar Ibn taimiyyah ba< bankawo maganar Sheikh Muhammad bn Abdulwahhab ba. a'a kawaifa cewa nayi Allah yace Annabi yace , ibn Abbas yace. Kuma ahaka nake kin annabi?.
Idan kace bana son annabi kokuma karya nake akan nafadi haka, to ai nana A'isha ma tafadi hakan itama batason annabi? Ko karya takeyi? Ga abinda tace:-
حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ يُوسُفَ حَدَّثَنَا سُفْيَانُ عَنْ إِسْمَاعِيلَ عَنْ الشَّعْبِيِّ عَنْ مَسْرُوقٍ عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ مَنْ حَدَّثَكَ أَنَّ مُحَمَّدًا صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَأَى رَبَّهُ فَقَدْ كَذَبَ وَهُوَ يَقُولُ {لَا تُدْرِكُهُ الْأَبْصَارُ}
Ma'ana:- nana A'isha tace "duk wanda yace maka annabi yaga Allah to karya yakeyi"
(bukhari 7380)
Wallahi tunda nana A'isha tafadi haka toh muma bazamuji kunyar karyata mutum ba muddin yace annabi yaga Allah> domin bazamu karyata A'isha ba kuma mu gaskata ka.
KAMMALAWA
Anan nakawo karshen wannan rubutun nawa. Sai mun hadu awani rubutun nagaba. Ina rokon Allah yasa abinda nayi na daidai nahadu ni da ku a ladan, wanda kuma nayi kuskure ina fatan Allah ya yafe min. kamar kullum; ina nan ina jiran tambaya, shawara, ko karin bayani daga wajenku.
Allah yasa mudace ameen.
Awaisu Haruna
Al'arabee
Fagge. ILIMIN GAIBU
Gabatarwa;
إن الحمد لله تعالى ، نحمده ونستعين به ونستغفره ، ونعوذ بالله تعالى من شرور أنفسنا وسيئات أعمالنا ، من يهد الله تعالى فلا مضل له ، ومن يضلل فلا هادي له ، وأشهد أن لا إله إلا الله وحده لا شريك له ، وأشهد أن محمداً عبده ورسوله .
أما بعد :
فإن أصدق الحديث كتاب الله تعالى وأحسن الهدي هدي محمد - صلى الله عليه وآله وسلم - ، وشر الأمور محدثاتها ، وكل محدثة بدعة ، وكل بدعة ضلالة ، وكل ضلالة في النار .
Bayan haka ina yiwa yan uwana musulmi sallama irin ta addinin musulunci; assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.
wannan rubutun zai kunshi magana ne akan wata mas'ala da data dade tana kewayawa kuma tana kawo rudani tsakanin al'umar musulmi. irin wadannan matsalolin suna da yawa kuma sun dade suna ci mana tuwo a kwarya amma har yanzu mun kasa gusar dasu ta hanyar da yadace saide kullum a tsaya ana ta kai kawo da faden bakake maganganu tsakanin wadanda suke da banbanci ra'ayi gamedasu.
Inda ace mu musulmi muna bin umarnin Allah da manzonsa sau da kafa da duk wadansu abubuwan na rikici basu same mu ba.
sabani yana yawan kawo mana rikici da rabuwar kai kuma bayan Allah yabamu hanyarda zamubi musami waraka idan wani sabani yakunno kai cikin mu.
Allah yace:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُولِي الْأَمْرِ مِنْكُمْ فَإِنْ تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إِلَى اللَّهِ وَالرَّسُولِ إِنْ كُنْتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ ذَلِكَ خَيْرٌ وَأَحْسَنُ تَأْوِيلًا
ma'ana: yaku wadanda sukayi imani kuyi biyayya ga Allah sannan kuyi biyayya ga manzonsa sannan kuyi biyayya ga malamai, idan kukayi sabani acikin wani abu toh ku maida hukunci zuwaga littafin Allah da hadisan manzon Allah indai kunyi imani da Allah da ranar lahira, hakan shine alkhairi gareku kuma shine mafi kyawun karshe.
(ibn abbas)
kunga kenan da ace idan mun samu sabani muna mayar dashi zuwaga littafin Allah da sunnah ta manzon Allah SAWbisa ga fassarar magabata na kwarai da rikice rikicen da suke faruwa tsakaninmu sun kau.
mas'alar da nakeson magana akanta itace 'ilimin gaibu'.
al'umar musulmi takasau kaso biyu gabeda ilimin gaibu, wasu sunce Allah ne kadai yasan gaibu, wasu kuma sunce ai manzon Allah SAW ma yasan gaibu. wasu ma har suke karawa dacewa shehunansu/ waliyyansu/imamansu sun san gaibu.
shiyasa yani nufin yin wannan rubutun domin na rubuta iyaka fahimtata da mas'alar bisa dogaro ga ayoyin Allah da hadisan manzon Allah sallallahu alaihi wasallam. ina fatan Allah yamin muwafaqa wajen rubuta dai-dai da yardarsa.
Allah yasa mudace.
SASHI NA FARKO
Menene gaibu?
ita dai kalmar gaibu kalma ce ta larabci. wadda take hawa kan duk abinda yabuyarwa sanin mutum.
duk abinda tunanin mai tunani ko hankalin mai hankali bazai iya riskarsa ba to shi ake cewa gaibu. misali:
sanin yaushe zaka mutu, sanin abinda zai sami rayuwarka anan gaba duk wadannan gaibu ne. sannan sanin ranar tashiin alkiyama duka suna daga cikin misalan gaibu.
SASHI NA BIYU
Allah ne kawai yasan gaibu.
Hakika akwai dalilai dayawa da sukazo domin su nuna mana cewa Allah ne kawai yasan gaibu, kuma banda shi babu wanda yasan gaibu.
zamu kawo kadan daga cikin ayoyin domin asamu tabbacin abinda muka fada. misali: Allah yace:
وَعِنْدَهُ مَفَاتِحُ الْغَيْبِ لَا يَعْلَمُهَا إِلَّا هُوَ
ma'ana: Allah yace; kuma awajesa(allah) mabudan ilimin gaibu suke, babu wanda yasansu sai shi(Allah).
kaga idan muka dubi ma'anar wanan ayar zamu gane cewa babu wanda yasan gaibu sai Allah. kadama kace mu yan izala mune muka fassara ayar ahaka, in kana shakka kaje ka duba duk wani tafsiri wanda duniya tayarda tafsiri ne zakaga irin abinda muka fada maka anan. kuma ba wannan ayar bace kawai take nuna hakan.
awani wajen ma Allah yace:-
قُلْ لَا يَعْلَمُ مَنْ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ الْغَيْبَ إِلَّا اللَّهُ وَمَا يَشْعُرُونَ أَيَّانَ يُبْعَثُونَ
ma'ana: kace musu(yakai annabi) babu wanda yasan gaibu a sama ko akasa sai Allah, kuma basu ma san yaushe kuma yaya za'a tashe suba.
Ma'ana: (Allah) *shine masanin gaibu, kuma babu wanda ya isa gaibun ubangiji ta bayyana gareshi, *saide wanda yaso daga cikin manzaninsa......
A karkashin wannan ayar akwai shubuhohi da suke bijirowa.
Wasu suna cewa toh ai wannan ayar ta nuna cewa manzanni sunsan gaibu
Amma gamai ido acikin alkur'ani da tafsiri da yaren larabci yasan ko kadan wannan ba haka yake ba.
Allah ya kore sanin gaibu ga kowa. Ayar yaga kuma sai tazo sa istisna'i tace saide wasu yardaddu daga cikin manzanni.
Toh anan wannan istisna'in shi ake cewa 'istisna'I munqadi'i', allazi yakunu mustasna laysa min jinsil mustasna minhu.
Ko kuma mu tambayi mai jayayya muce masa, shin su manzanni suna iya sanin abu tun kafin Allah yasanar dasu??? Kowa zai iya amsawa cewar a'a, kaga kenan kafin Allah yasanar dasu basu sani ba, toh kuwa indai basu sani ba kafin asanar dasu kenan basusan gaibu ba.
Idan karike ma'anarda nabayar abaya gameda gaibu, to zaka tuno cewa gaibu shine duk abinda ya buyarwa saninka.
Zai iya yiwuwa wani abun yazama gaibi awajena amma awajenka ba gaibu bane.
Misali; in nafito daga gida kasan menene a aljihuna??? A'a, amma aini na sani ko?? Eh. Toh kaga kai gaibu ne awajenka amma ni awajena ba gaibu bane.
Toh idan Allah ya sanar da manzonsa wani abu, toh shi wannan manzon abin ba gaibu bane awajensa. Mukuma mabiya gaibu ne awajenmu kafin annabin yasanar damu, amma dazarar an sanar damu to abin yazama ba gaibu ba tunda bai buyarwa saninmu ba.
Awata ayar kuma Allah yace:
تِلْكَ مِنْ أَنْبَاءِ الْغَيْبِ نُوحِيهَا إِلَيْكَ مَا كُنْتَ تَعْلَمُهَا أَنْتَ وَلَا قَوْمُكَ مِنْ قَبْلِ هَذَا
Ma'ana: (bayan Allah yakawowa annabi SAW kissoshin annabawa sai yace) duk wadannan suna daga cikin labaran gaibu muke maka wahayinsu a yanzu, da can dakai da mutanenka duk baku sani ba kafin ayi muku wahayin.
Ma'ana: (bayan Allah yakawowa annabi SAW kissar nana maryamu sai yace) duk wadannan suna daga cikin labaran gaibu muke maka wahayinsu a yanzu, domin baka cikinsu a lokacinda suke jefa kuria domin daukar renon maryam, kuma baka cikinsu lokacinda suke jayayya
Kafin in cigaba, yakamata in danyi tanbihi akan wadannan ayoyin guda biyu.
Wani. Zai iya fahimtarsu. A baibai, yace toh ai gashi ance an sanarda annabi gaibu, toh ai in baka manta ba a bayan munce duk abinda ya buya ga saninka shi ake cewa gaibu, amma da an sanar dakai toh ya tashi daga gaibu.
Ai da annabi baisan labarin nasu ba kenan, sai da akayi masa wahayi sannan yasani, toh ai tunda aka sanar dashi toh da abin gaibu ne amma da aka sanar dashi sai labarin yabar gaibu.
Wani mai taurin kan zai iya cewa shidai bai yarda ba domin ai ance. 'Anba'il gaibi' sai muce toh indai kuwa hakane toh duk musulmi kowa yasan gaibu, ina kace saboda me? Sai ince maka saboda ai ayar cewa tayi 'anta wa qaumaka' wato dakai da mutanenka, kaga kenan inhar katafi a haka zaka sami matsala.
Ma'ana: (Allah yacewa Annabi yafadawa mutane cewa) ban ce muku taskokin Allah a hannuna suke ba, sannan kuma bansan gaibu ba
Muna samun mutane masu musu, sai mukawo dalilai sai suce wai muje muyi karatu batareda wata hujja ba.
Yanzu wannan ayar kiri-kiri tafada Allah yasaka annabi yace baisan gaibu ba. Toh mai kakeso ace maka kuma???
Allah ya sauwake.
Ma'ana: kace musu bana iya amfanarda kaina haka kuma bana iya kore cutarwa in tazo min saide abinda Allah yaso, DA ACE NASAN GAIBU toh dana yawaitawa kaina alkhairi kuma da ban bari sharri ya sameni ba.
Itama wannan ayar ta bayyana mana abinda muka fada abaya.
Amma acikin ayar akwai inda annabi yace 'dana yawaitawa kaina alkhairi dakuma ban bari sharri yasameni ba'
Wannan akwai sashi guda da naware masa, kaidai kawai kacigaba da kasancewa dani.
Allah yasa mudace.
Toh tunda nakawo ayoyi yanzu kuma bari na juya bangaren hadisai
حدثنا أبو بكر بن أبي شيبة . حدثنا وكيع . حدثنا هشام بن عروة عن أبيه عن زينب بنت أم سلمة عن أم سلمة قالت قال رسول الله صلى الله عليه و سلم : ( إنكم تختصمون إلي وإنما أنا بشر . ولعل بعضكم أن يكون ألحن بحجته من بعض . وإنما أقضي لكم على نحو مما أسمع منكم . فمن قضيت له من حق أخيه شيئا فلا يأخذه . فإنما أقطع له قطعة من النار
يأتي بها يوم القيامة
Ma'ana:- Annabi SAW yace: lallai kukanzo wajena yayinda kuke jayayya, nikuma mutum ne, watakila dayanku yafi dayan iya bayanin hujja (koda kuwa bashi bane mai gaskiya), domin inamuku hukunci ne da abinda ya bayyana gareni da dalili, (toh kusani cewa) duk wanda yayarda na dauki hakkin dan uwansa nabashi toh kada ya amsa domin wani yanki ne na wuta nabashi, kuma saiyazo da abin a ranar kiyama.
Kasan dai babu yadda za'ayi Annabin rahama ya dauki hakkin wani yabawa wani alhali yana sane. Kawai yana hukunci ne da abinda bayani ya bijiro masa dashi, amma baya sanin abinda yake cikin zuciyar mutum. Shikuwa abinda yake cikin zuciya gaibu ne ga wanda ba mai zuciyar ba.
Awani hadisin kuma akace:
عن بن عمر قال قال رسول الله صلى الله عليه و سلم : مفاتيح الغيب خمس لا يعلمها إلا الله................ .................... ............
Ma'ana: Annabi sallallahu alaihi wasallam yace : mabudai na ilimin gaibu guda biyar ne, babu wanda yasansu sai Allah.---------------
(sunan nasa'i. (11258)
Kaji fah shugaban masu gaskiya! Gashi dai annabi yace babu wanda yasani sai Allah. In kace min karya nake in nace annabi baisan gaibu ba toh Annabi kafadawa, domin maganar ba tawa bace ta Allah da annabin ce, ni dan dakone kawai.
Yakamata mu dinga yadda da duk abinda Allah da manzonsa suka fada.
to bayan wadannan bayanan nawa sai kuma wani abu daya shafi wannan lamarin.
Duk yayinda muka fito mukayi irin wannan bayanin sai wadanda suke ganin ba dai-dai bane sudinga zarginmu da cewa wai bama son annabi. subhanallah! kenan yanzu mu arna ne? domin kuwa duk wanda baya son abai rne ne. tayayaa bamu son annabi kuma har muke kafa hujja da maganganunsa ingantattu?
Haba dan uwa! bafa mune mukace bausan gaibu ba, Allah ne yafada kuma shima yafada, toh sokake muce karya ne ayoyin da hadisan?
malamanku fa gwanaye wajen fadar falala da fifiko da darajar ma'aiki sallallahu alaihi wasallam. kai kasani nima nasani cewa dani dakai da malamina da malaminka da shehu na da sheunka da waliyyina da waliyyinka da imami na da imaminka da da da da da da duk bamu isa mu kididdige matsayin annabi ba.
Toh dan kace baisan gaibu ba rage masa matsayi kayi? wallahi ba haka bane, babu abinda zai ragu acikin darajar annabi don kace baisan gaibu ba.
idan kace banason annabi don nace baisan gaibu ba to ai bani kadai bane nafadi hakan.
idan kakoma cikin sahih muslim hadisi ta tabbata daga nana a'isha yardar allah taara tabbatuwa akanta. ita wannan shine fatawarta. ga hadisin kamar haka:-
حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ يُوسُفَ حَدَّثَنَا سُفْيَانُ عَنْ إِسْمَاعِيلَ عَنْ الشَّعْبِيِّ عَنْ مَسْرُوقٍ عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ مَنْ حَدَّثَكَ أَنَّ مُحَمَّدًا صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَأَى رَبَّهُ فَقَدْ كَذَبَ وَهُوَ يَقُولُ {لَا تُدْرِكُهُ الْأَبْصَارُ} وَمَنْ حَدَّثَكَ أَنَّهُ يَعْلَمُ الْغَيْبَ فَقَدْ كَذَبَ وَهُوَ يَقُولُ لَا يَعْلَمُ الْغَيْبَ إِلَّا اللَّه
ma'ana: nana a'isha tace "duk wanda yace maka annabi yaga allah toh karya yakeyi, sannan duk wanda yace maka annabi yasan gaibu to karya yakeyi. domin shi din yana cewa babu wanda yasan gaibu sai allah ".
(sahihu bukhari 7380,6945. sahih muslim 457, 287)
allahu akbar, allahu akbar, allahu akbar
nasan dai ko kacemin karya nake to zakaji kunya kace nana aisha karya takeyi domin tafika sanin annabi kuma tafika son annabi.
ko kuma zakace hadisin da'ifi ne?
haba dan uwa! kar kabari masu ilimi sumaka dariya mana, tayaya zakaga hadisi a bukhari da muslim sannan kace da'ifi ne? ai gara karma kafara.
zan rufe ne da wani hadisi na manzon allah salllallau alaihi wasallam daya nuna cewa baisan gaibu ba. ga hadisin:-
حدثنا مسدد ثنا بشر عن خالد بن ذكوان عن الربيع بنت معوذ بن عفراء قالت
: جاء رسول الله صلى الله عليه و سلم فدخل علي صبيحة بني بي ( البناء الدخول بالزوجة ) فجلس على فراشي كمجلسك مني فجعلت جويريات يضربن بدف لهن ويندبن من قتل من آبائي يوم بدر إلى أن قالت إحداهن وفينا نبي يعلم ما في الغد فقال " دعي هذه وقولي الذي كنت تقولين " .
ma'ana: (wata rana annabi ya shiga wani gida, da wata mata taganshi sai tace) acikinmu akwai annabin allah wanda yasan abinda zai faru gobe(gaibu), sai annabi yace tadena fadun haka, amma tacigaba da waccan maganar tata tada.
wannan shima dalili ne dayake nuna cewa manzonmu bai san gaibu ba.
Kammmalawa
yakai dan uwa kasani cewa ba kin manzon Allah mukeyi ba, kawai dai muna so mufito da addinin Allah nr kamar yadda Allah yasaukar dashi kuma ya aiko annabinsa yamana bayanin addinin, kuma babu shakka annabi ya isar da sakond Allah ya aiko shi dashi. Toh mai zai hana in dena bin ra'ayi na dana malamina kaima kadena bin ra'ayinka dana malaminka duk m ukoma kan malamin kowa da kowa manzon Allah sallallahu alaihi wasallam.
Anan nakawo karshen wannan rubutun nawa.
Abinda nayi daidai Allah yahadani ni daku acikin ladan, wanda kuma nayi kuskure ina fata allah zai gafarta min.
ina nan ina jiran gyara, shawara ko tambaya daga waen yan uwana musulmi.
Wassalamu alaikum warahmatullati ta'ala wabarakatuhu.
Allah yasa mudace.
Awaisu haruna
Al'arabee
Fagge
AL'ARSHI
Gabatarwa:-
إن الحمد لله تعالى ، نحمده ونستعين به ونستغفره ، ونعوذ بالله تعالى من شرور أنفسنا وسيئات أعمالنا ، من يهد الله تعالى فلا مضل له ، ومن يضلل فلا هادي له ، وأشهد أن لا إله إلا الله وحده لا شريك له ، وأشهد أن محمداً عبده ورسوله .
أما بعد :
فإن أصدق الحديث كتاب الله تعالى وأحسن الهدي هدي محمد - صلى الله عليه وآله وسلم - ، وشر الأمور محدثاتها ، وكل محدثة بدعة ، وكل بدعة ضلالة ، وكل ضلالة في النار .
Bayan haka ina yiwa yan uwana musulmi na wannan shafi mai albarka sallama irinta addinin musulunci assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wabarakatuhu.
Bayan haka;
Wannan rubutu mai take irin wanda kuka gani asama zai kunshi wasu bayanai ne masu muhimmanin gaske musamman awannan zamanin da ilimi yafara yankewa daga tunanin al'umma. Yawanci idan wani abu yataso mana bama tunanin tayaya zamu kautar da rudanin da yake cikinsa tahanyar ilimi. Saide ayi kaikawo awaje daya anata bayarda misalai nahankali kai wasu ma basu dace da hankalin ba wallahi.
Yakamata duk abinda yatunkaremu muyi kokarin saka ilimi acikinsa domin shine dan gari kuma shine zai iya gano mana hanyar da zamubi domin fita daga cikin batan da muce ciki ayanzu.
Toh menene illimi?
Ga abinda imamush-shafi'I yafada gameda ilimi:-
وقال الشافعي رحمه الله تعالى :
كل العلوم سوى القرآن مشغلة
إلا الحديث وإلا الفقه في الدين
العلم ما كان فيه قال : حدثنا
وما سوى ذاك وسواس الشياطين
Ma'ana; imamu shafi'iy yace
-dukkan iliminda ba qur'ani ba toh kayan shagaltarwa ne
-saide ko hadisi ko fiqhun addini
-shi ilimi shine abinda akace haddasana acikinsa
-duk abinda ba wannan ba yazama waswasin shaidanu.
Shikuma ibn qayyum aljauziyyah yace:-
وقال ابن القيم رحمه الله تعالى :
العلم قال الله قال رسوله
قال الصحابة هم أولو العرفان
Ma'ana; ibnul qayyum yace;
-shi ilimi shi ne Allah yace Annabi yace
-sahabbai sunce( domin sune mafi sani ga abinda Allah yace ko Annabi yace).
Tanan zaku gano kwarewa da azamcinmu damukace zamuyi addinine tahanyar kitabu(qur'ani) was-sunnah(hadisi) ala manhaji salafussaleh. (sahabbai da tabi'ai da duk wanda fassararsa tayi daidai da tasu).
Kaga kenan idan wani abu yashige mana duhu sai mu warware shi tahanyar ilimi. Dama ai Allah yace;
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُولِي الْأَمْرِ مِنْكُمْ فَإِنْ تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إِلَى اللَّهِ وَالرَّسُولِ إِنْ كُنْتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ
Ma'ana; yaku wadanda sukayi imani kuyiwa Allah biyayya sannan kuyiwa manzon Allah biyayya sannan kuyiwa malamai/shugabanni biyayya. Idan kukayi sabani toh kukoma zuwaga Allah (qur'ani) da manzonsa (hadisi) indai kunyi imani da Allah da ranar karshe.
Awannan rubutu nawa zanyi maganane akan mas'alar 'DAIDAITUWAR ALLAH AKAN AL'ARSHINSA'.
Sanin kowane cewa wannan dayace daga cikin mas'alolin da suka dade kuma har yanzu suna kaikawo tsakanin al'ummar musulmi mabanbanta.
Alal hakika idan akace za'a kalli mas'alar a mahanga ta ilimi toh bata da wahalar warwarewa.
Ina fatan Allah zaimin muwafaka acikin rubutuna. Allah yasa mudace ameen.
SASHI NA FARKO
A ina al'arshi take?
Kafin mushiga bayani kai tsaye gameda gameda cewa shin Allah madaukaki ya daidaita akan al'arshi ne kokuwa a'a, yakamata mufara sanin ita kanta al'arshin a ina take.
Kamar yadda ya tabbata a hadisi ingantacce, hakika ita al'arshi a saman sama take. Hakan yazo ne awani hadisi dazan kawo.
Ga hadisin:-
حدثنا زكريا بن يحيى الساجي ثنا هدبة بن خالد ثنا حماد ابن سلمة عن عاصم عن زر عن ابن مسعود أنه قال : ما بين السماء الدنيا والتي تليها مسيرة خمس مئة عام ومابين كل سماء مسيرة خمس مائة عام وما بين السماء السابعة والكرسي مسيرة خمس مئة عام وما بين الكرسي والماء مسيرة خمس مئة عام والعرش على الماء والله عز و جل على العرش يعلم ما أنتم عليه
Ma'ana:- tsakanin saman duniya da wadda take bimata tafiyar shekara dari biyar ne, tsakanin kowace sama da wadda take bi mata tafiyar shekara dari biyar ne. tsakanin sama ta bakwai da kursiyyi tafiyar shekara dari biyar ne, tsakanin kursiyyi da ruwanda yake sama shima tafiyar shekara dari biyar ne, ita kuma al'arshi tana kan ruwan, shikuma Allah yanakan al'arshi.
(mu'ujamul kabir 8987)
Idan muka dubi wannan hadisin zamu ga cewa hakika al'arshi tana saman ruwanda yake a saman kursiyyi ita kuma kursiyyi tana saman sama ta bakwai ahaka har kayo kasa.
Awani hadisin kuma akace:-
وعن العباس بن عبد المطلب - رضي الله عنه - قال: قال رسول الله - صلى الله عليه وسلم -: (هل تدرون كم بين السماء والأرض؟) قلنا: الله ورسوله أعلم قال: (بينهما مسيرة خمسمائة سنة، ومن كل سماء إلى سماء مسيرة خمسمائة سنة وكثف كل سماء خمسمائة سنة، وبين السماء السابعة والعرش بحر بين أسفله وأعلاه كما بين السماء والأرض، والله - سبحانه وتعالى - فوق ذلك، وليس يخفى عليه شيء من أعمال بني آدم)
Ma'ana: annabi sallallahu alaihi wasallam yace:- shin kunsan adadin nisan dayake tsakanin sama da kasa? Sai sahabbai sukace ai Allah da manzonsane suka sani. Sai annabi yace:- tazararsu nisan tafiyar shekara dari biyar ce, sannan daga kowace sama zuwa samanda take biye da ita shima nisan tafiyar shekara dari biyar ne, tsakanin samata bakwai da al'arshi kuma wani kogine, nisan dayake tsakanin saman kogin da kasan sa kamar nisan dayake tsakanin sama da kasa ne. shikuma Allah madaukaki yana saman haka(al'arshi) amma duk da haka ayyukan bani adam basa buya agareshi.
Shima wannan hadisin yakara tabbatar mana da cewa al'arshi a asaman sama take.
SASHI NA BIYU
A'ina Allah yake?
Babbar magana! Akan amsar wannan tambayar ne al'umar musulmi suke ta kaikawo.
Amma magana sahihiya itace Allah yana saman (al'arshi).
Yawanci muna cewa Allah yana sama, amma ba muna nufin asama ta daya ko ta biyu har zuwa ta bakwai ba, muna nufin yana al'arshi, toh amma dayake ita kanta al'arshin a saman sama take ba laifi bane don kace yana sama indai ba kana nufi sama daya-sama ta bakwai ba.
Toh menene dalili gameda cewa Allah yana sama?
Wallahi dalilanmu sunfi gaban lissafi game da fadin hakan.
Sanin kowa ne cewa dalilai kala biyu ne, akwai dalili na shari'ah sannan akwai dalili na hankali. Dukkansu kuma muna dasu domin tabbatar da wannan aqidar.
Kamar yadda muka samu daga magabata cewa ana kafa hujjah ne a musulunci da abubuwa guda uku.
a)alkur'ani mai girma
b)ingantaccen hadisin Annabi
c)ijma'in malaman musulunci.
Zanyi amfani wadannan makaman domin yakar gurguwar akidarnan tacewa Allah yana ko ina.
Zan fara da kawo dalilai na ilimi/shari'ah sannan daga baya nakawo na hankali.
Acikin alkur'ani mai girma ayoyi dayawa sun tabbatar mana cewa Allah yana sama. Ga misali:
إِنَّ رَبَّكُمُ اللَّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ
Ma'ana: hakika ubangijinku shine Allah wanda yahalicci sammai da kassai acikin kwana shida sannan ya daidaita akan al'arshi.
Wannan ayar ta tabbatar mana da cewa Allah yana al'arshi (sama).
Saboda ubangiji yanaso yabamu tabbaci akan wannan maganar saida yamaimaita fadin haka da wannan usulubin na (اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ) sau bakwai. Zan kawosu ajere tareda fadin sunan sura da aya. batareda fassarawa ba saboda duk abu aya suke nunawa. Allah yace:-
إِنَّ رَبَّكُمُ اللَّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى ال?ْعَرْشِ يُدَبِّرُ الْأَمْرَ مَا مِنْ شَفِيعٍ إِلَّا مِنْ بَعْدِ إِذْنِهِ ذَلِكُمُ اللَّهُ رَبُّكُمْ فَاعْبُدُوهُ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
(yunus aya ta 3)
اللَّهُ الَّذِي رَفَعَ السَّمَاوَاتِ بِغَيْرِ عَمَدٍ تَرَوْنَهَا ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ وَسَخَّرَ الشَّمْسَ وَالْقَمَرَ كُلٌّ يَجْرِي لِأَجَلٍ مُسَمًّى يُدَبِّرُ الْأَمْرَ يُفَصِّلُ الْآيَاتِ لَعَلَّكُمْ بِلِقَاءِ رَبِّكُمْ تُوقِنُونَ
(ra'ad aya ta 2)
الرَّحْمَنُ عَلَى الْعَرْشِ اسْتَوَى
(daha aya ta 5)
الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ الرَّحْمَنُ فَاسْأَلْ بِهِ خَبِيرًا
(furqan 59 )
اللَّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ مَا لَكُمْ مِنْ دُونِهِ مِنْ وَلِيٍّ وَلَا شَفِيعٍ أَفَلَا تَتَذَكَّرُونَ
(sajdah 4)
هُوَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ يَعْلَمُ مَا يَلِجُ فِي الْأَرْضِ وَمَا يَخْرُجُ مِنْهَا وَمَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وَمَا يَعْرُجُ فِيهَا وَهُوَ مَعَكُمْ أَيْنَ مَا كُنْتُمْ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ
(hadid 4 )
Wadannan guda shida kenan idan ka hada da wadda nakawo ta farko zaka samu jerin ayoyi bakwai kenan dasuke nuna cewa Allah ya daidaita akan al'arshinsa.
Don ma kada kace mu ahlussunnah mune muka fassara ayar ahaka bari mukawo maka abinda ibn kathir yafada gameda fassarar ayar.
وأما قوله تعالى: { ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ } فللناس في هذا المقام مقالات كثيرة جدا، ليس هذا موضع بسطها، وإنما يُسلك في هذا المقام مذهب السلف الصالح: مالك، والأوزاعي، والثوري، والليث بن سعد، والشافعي، وأحمد بن حنبل، وإسحاق بن راهويه وغيرهم، من أئمة المسلمين قديما وحديثا، وهو إمرارها كما جاءت من غير تكييف ولا تشبيه ولا تعطيل. والظاهر المتبادر إلى أذهان المشبهين منفي عن الله، فإن الله لا يشبهه شيء من خلقه،
Malam ibn kathir yace:-awajen fassarar akwai maganganu dayawa na mutane wajen fassararta wanda ba muhallinshi bane nan. Amma dai abinda yakamata shine irin maganarda magabata nakwarai suka fada akanta; kamarsu imamu malik, auza'I, safiyanus-sauriy, laiys bin sa'ad,imamu shafi'i, imamu ahmad bin hanbal, ishaq bin rahuyah da sauransu. Sukace wannan ayar kawai za'a fassarata ne a yanda tazo batare da fadin yaya ya dedeta ba ko fadin kamanceceniya gameda hakan kokuma canja ma'anarta zuwa wani abin nadaban.
Kaga kenan duk wadannan malaman sunada fatawar cewa Allah yana sama.
Duk dayake dai a kwanakin baya naji wani malami agarin mu dayake cewa ai kalmar istiwa'I anan tana nufin 'istaula' ne.
Haba akramakallah! Ai wannan bayanin ba nan bane muhallinsa.
Sanin duk wani mai mu'amala da kalmominda suke a cikin al'qur'an ne cewa kalmar 'istiwa tana zuwa ne a yanayi guda uku.
Na farko. Tana zuwa abiye da ((علي toh indai tazo da ahaka tana nufin daidaituwar wani abu asaman wani abu.
A yanayi na biyu kuma tana zuwane abiye da kalmar (إلى) toh idan tazo da wannnan yanayin tana matsayinn nufi ne. kamar ace mutum yayi nufin yin wani abu.
Misali;-
ثُمَّ اسْتَوَى إِلَى السَّمَاءِ وَهِيَ دُخَانٌ فَقَالَ لَهَا وَلِلْأَرْضِ ائْتِيَا طَوْعًا أَوْ كَرْهًا قَالَتَا أَتَيْنَا طَائِعِينَ
Ma'ana; (ayar bayanta tayi bayani akan yadda Allah yayi tsarin gina kasan duniya. Bayan yagama ginin kasa) sai yayi nufin sama (ginin halittarta) alokacin tana hayaki……………
Akaro na uku kuma tana zuwa ne a matsayinta na kalma mai zaman kanta. To idan tazo da wannan ma'anar tan nufin cikar hankali akan wani mutum.
Misali:-
وَلَمَّا بَلَغَ أَشُدَّهُ وَاسْتَوَى آتَيْنَاهُ حُكْمًا وَعِلْمًا
Ma'ana: yayinda yacika shekara arba'in kuma hankalinsa yacika sai muka bashi ilimi da annabta.
Wadannan sune yanayi guda uku da wannan kalmar take zuwa dasu kuma kowacce mun bayarda ma'anarta. Babu wata ma'ana ta hudu da wannan kalmar take dauka. Kenan idan muka dubi a siffarda kalmar tazo acikin ayoyin da muka kawo zamuga cewar tana nufin Allah ya daidaita akan al'arshinsa.
Toh kaddara ma ace malamin ya rinjayemu akan wannan ayar. To ai akwai wadansu ayoyin sunfi cikin buhu dasuke nuna cewa Allah yana sama, kuma bada wannan samfirin kirar sukazo ba. kowacce tazo ne da irin nata usulubin. Zanyi ta kawo su har iyaka inda ganaji domin wallahi nima bansan iyakar yawansu ba, saboda ban taba zama domin na kididdige suba. Ga ayoyin kamar haka:-
Allah yace:-
أَأَمِنْتُمْ مَنْ فِي السَّمَاءِ أَنْ يَخْسِفَ بِكُمُ الْأَرْضَ فَإِذَا هِيَ تَمُورُ
Ma'ana: shin yanzu kun aminta akancewa wanda yake sama(Allah) bazai iya kifar da kasarsu ba?.
Toh abin tambaya anan shine waye wanda yake sama?
Amsa; Allah ne wanda yake sama
Toh waye yace Allah yana sama?
Allah shine yace yana sama.
Ga aya tagaba.
أَمْ أَمِنْتُمْ مَنْ فِي السَّمَاءِ أَنْ يُرْسِلَ عَلَيْكُمْ حَاصِبًا فَسَتَعْلَمُونَ كَيْفَ نَذِيرِ
Ma'ana: ko kun amintune akan cewa wanda yake sama bazai iya aiko muku da duwatsu na azaba ba?………..
Itama wannan ayar tana nuna mana cewa Allah yana sama.
Bari mukai ziyara zuwa tafsirin wanda yafi kowa iya tafsiri a duniya wato Abdullahi ibn Abbas domin muga mai yace gameda wadannan ayoyin guda biyu.
Ga abinda malam ibn Abbas yace:-
{ أَمْ أَمِنتُمْ مِّن فِي السمآء } عذاب من في السماء على العرش إذ عصيتموه { أَن يُرْسِلَ عَلَيْكُمْ حَاصِباً }
Ma'ana: shin yanzu kun amintu akan cewawanda yake sama akan al'arshi(Allah) idan kuka saba masa bazai iya aiko muku da ruwan duwatsuba?
Anan kenan menene fatawar ibn Abbas?
Amsa: fatawarshi shine Allah yana al'arshi.
Sannan awata ayar kuma Allah yace:-
إِلَيْهِ يَصْعَدُ الْكَلِمُ الطَّيِّبُ وَالْعَمَلُ الصَّالِحُ يَرْفَعُهُ
Ma'ana: izuwa ga Allah ne tsarkakan kalmomi(kalmatush-sh ahada) suke hauhawa sannan kyawawan aiyuka ma izuwa gareshi suke daukakuwa.
Anan kaga hauhawa tana nufin abu yatashi daga kasa zuwa sama. sannan itakanta kalmar 'irtifa'i' tana nufin daukakar abu daga kasa zuwa sama. Haka yake a ka'idar larabci sannan haka yake a cikin tafsirai idan ka duba.
Awata ayar kuma Allah yace:-
تَعْرُجُ الْمَلَائِكَةُ وَالرُّوحُ إِلَيْهِ فِي يَوْمٍ كَانَ مِقْدَارُهُ خَمْسِينَ أَلْفَ سَنَةٍ
Ma'ana: mala'iku suna hauhawa izuwa gareshi tareda jibrilu awuni daya, alhalin asalin nisan tafiyar ga wanda ba mala'ika ba nisan tafiyar shekara dari biyar ne.
Ance mala'iku suna hauhawa. Toh tambaya anan shine; daga ina zuwa ina?
Amsa: daga kasa zuwa sama.
Awata ayar kuma Allah yace:-
يَخَافُونَ رَبَّهُمْ مِنْ فَوْقِهِمْ وَيَفْعَلُونَ مَا يُؤْمَرُونَ
Ma'ana: su (mala'iku) sunajin tsoron ubangijinda yake a samansu (al'arshi) sannan suna aikata duk abinda ya umarce su.
Fadin cewa ubangijinda yake saman su hakan yana tabbatarda abinda muka fada abaya na cewa al'arshi tana saman ruwa ne shikuma ruwa yana saman kursiyyi. Ita kuma kursiyyi tana saman sama ta bakwai.
Sannan dama ai sanannen abu ne cewa hatta shugaban mala'iku gaba daya wato jibrilu shikansa iyakacinsa shine sidratul muntaha. Zakasamu hakan a hadisin dayazo na isra'I da mi'iraji.
Allahu akbar! Abin mamaki! Wallahi fir'auna ma ya yarda Allah yana sama. Ga ayarda tanuna haka:
وَقَالَ فِرْعَوْنُ يَا أَيُّهَا الْمَلَأُ مَا عَلِمْتُ لَكُمْ مِنْ إِلَهٍ غَيْرِي فَأَوْقِدْ لِي يَا هَامَانُ عَلَى الطِّينِ فَاجْعَلْ لِي صَرْحًا لَعَلِّي أَطَّلِعُ إِلَى إِلَهِ مُوسَى وَإِنِّي لَأَظُنُّهُ مِنَ الْكَاذِبِينَ
Ma'ana: fir'auna yace yaku yanfada nidai bansan kuna da wani ubangijiba bayan ni, saboda haka yakai hamana ku ginamin matattakala mai karfi wadda zanje ingano ubangijinda musa yace min yana sama, ni dai ina tsammanin musa yana cikin makaryata gameda cewa akwai wani Allah a sama wanda ba niba.
Awata samfirin ayar mai kama da wannan kuma Allah yace:-
وَقَالَ فِرْعَوْنُ يَا هَامَانُ ابْنِ لِي صَرْحًا لَعَلِّي أَبْلُغُ الْأَسْبَابَ (36) أَسْبَابَ السَّمَاوَاتِ فَأَطَّلِعَ إِلَى إِلَهِ مُوسَى وَإِنِّي لَأَظُنُّهُ كَاذِبًا
Ma'ana: fir'auna yace yakai hamana inaso kagina min wata matattakala domin in tafi sararin sama* *zanje sararin ne domin naleka nagani shin da gaskene musa yanada Allah asama wanda ya aiko shi?
Awata ayar kuma Allah yace:
يا عيسى إني متوفيك ورافعك إلي
Ma'ana:- Allah yacewa annabi Isah hakika zan dauki ranka sannan zan dakake ka izuwa sama wajena.
Awata ayar mai kama da wannan kuma Allah yace:-
وَمَا قَتَلُوهُ يَقِينًا (*) بَلْ رَفَعَهُ اللَّهُ إِلَيْهِ وَكَانَ اللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمًا
Ma'ana: (Allah yace gameda kafirai masu karyarcewa sun kashe annabi Isa,)basu kasheshi ba abisa yakini kawai dai Allah ya daukakeshi (sama)ne izuwa, wajensa. Hakika Allah mabuwayi ne kuma mai hikima ne.
Inda zaka tambayi mai tambaya cewa a yanzu ina annabi isah yake kowa zaice maka yana sama. Toh kuma Allah yace izuwa wajensa, kenan Allah yana ina? Yana sama.
Awata ayar kuma Allah yace:-
يدبر الأمر من السماء إلى الأرض
Ma'ana: (Allah) yana jujjuya al'amura daga sama zuwa kasa.
Awata ayar kuma Allah yace:-
تنزيل الكتاب من الله العزيز الحكيم
Ma'ana; (shi alkur'ani) saukakken littafi ne daga mabuwai mai hikima (Allah)
Ance Allah yasaukar da kur'ani, idan akace ansaukar da abu ana nufin daga sama zuwa kasa ne ko daga kasa zuwa sama?
Amsa: daga sama ne zuwa kasa. Kenan wanda yasaukar dashi yana ina? Yana sama kenan
Yanzu abinda zai kara nuna mana cewa Allah yana sama shine wani hasidi ingantacce, ga hadisn kamar haka:-
عن سعيد بن المرزبان عن عكرمة عن ابن عباس رضي الله عنه قال جاء رجل الى النبي صلى الله عليه و سلم ومعه جارية أعجمية سوداء فقال على رقبة فهل تجزيء هذه عني فقال أين الله فأشارت بيدها إلى السماء فقال من أنا فقالت أنت رسول الله قال اعتقها فانها مؤمنة
Ma'ana:- Abdullahi bin Abbas yace; wata rana wani mutum yazo wajen Annabi sallallahu alaihi wasallam atare dashi akwai kuyangarsa bakar fata, sai ya tambayi annabi gameda yanta baiwa yace wannan idan na yanta wannan kuyangartawa ya isarmin?
Sai annabi ya tanbayeta yace mata a ina Allah yake? Sai tanuna dan yatsanta sama tace yana sama, sai annabi yace mata toh ni waye?
Sai tace kai manzon Allah ne, sai annabi yacewa mutumin kaje ka yanta ta domin mumina ce.
(dala'ilut-tauhid)
Toh ai kasan dai ba'ayin kuskure agaban annabi kuma yayi shiru, kuma shine ya tambaye ta kuma tace Allah yana sama, sannan kuma annabi yace a yanta ta saboda wannan amsarda tabada harma yamata shaida akan cewa mumina ce.
Awani hadsin kuma akace:-
أَخْبَرَنَا أَبُو طَاهِرٍ الْفَقِيهُ ، أَخْبَرَنَا أَبُو حَامِدِ بْنُ بِلالٍ ، حَدَّثَنَا عَبْدُ الرَّحْمَنِ بْنُ بِشْرِ بْنِ الْحَكَمِ بْنِ حَبِيبِ بْنِ مِهْرَانَ الْعَبْدِيُّ ، حَدَّثَنَا سُفْيَانُ بْنُ عُيَيْنَةَ ، عَنْ عَمْرِو بْنِ دِينَارٍ ، عَنْ أَبِي قَابُوسَ ، مَوْلًى لِعَبْدِ اللهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ الْعَاصِ ، عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ الْعَاصِ ، رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا ، قَالَ : إِنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ، قَالَ : الرَّاحِمُونَ يَرْحَمُهُمُ الرَّحْمَنُ ، ارْحَمُوا مَنْ فِي الأَرْضِ يَرْحَمْكُمْ مَنْ فِي السَّمَاءِ
Ma'ana; annabi yace:- Allah(mai rahama) yana jinkan masu tausayi akan bayinsa, kujikan wadanda suke kasa sai wanda yake sama yajikanku.
(baihaqi 893)
Wannan hadisin ai nasan kasanshi abakin kowa da kowa. Toh abin tambaya ana shine wanene wanda yake sama? Dole kace Allah tunda shi kadaine mai ikon yin rahama ga bayinsa. Sannan tambaya tagaba shin waye yafadi maganar? Dole kace annabi ne yafada. Tunda kuwa annabi ne yafada to mu mun yarda da cewa Allah yana sama kamar yadda muka samu tabbaci.
Awani hadisin kuma akace:-
وأخبرنا القاسم بن جعفر قال ثنا محمد بن أحمد بن عمرو قال ثنا سليمان بن الأشعث قال ثنا يزيد بن خالد بن موهب الرملي قال ثنا الليث بن سعد عن زياد بن محمد عن محمد بن كعب القرضي عن فضالة بن عبيد عن أبي الدرداء قال
سمعت رسول الله صلى الله عليه و سلم يقول من اشتكى منكم شيئا أو اشتكى أخ له فليقل ربنا الله الذي في السماء.............. ....
Ma'ana: annabi yace:- wanda wani abu yake damunsa kokuma yake damun dan uwansa toh idan zaiyi addu'ah sai yace 'ya ubangijinmu wanda yake sama'…………….
(ikhfa'it-tashkil)
Awani hadisin kuma akace:-
فقال النبي صلى الله عليه و سلم:....... إنه لفوق سماواته على عرشه
Ma'ana: annabi yace:…………. Ai shi Allah yana saman sama akan al'arshinsa.
(asma'u wassifat na baihaqiy)
Awani hadisin kuma akace:-
وَأَخْبَرَنَا عَلِيُّ بْنُ أَحْمَدَ بْنِ عَبْدَانَ ، أَخْبَرَنَا أَحْمَدُ بْنُ عُبَيْدٍ ، حَدَّثَنَا الْحَسَنُ بْنُ الْمُتَوَكِّلِ ، حَدَّثَنَا سَهْلٌ ، عَنْ أَبِي مُعَاوِيَةَ ، عَنْ شَبِيبِ بْنِ شَيْبَةَ ، عَنِ الْحَسَنِ ، عَنْ عِمْرَانَ بْنِ حُصَيْنٍ ، رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ ، قَالَ : قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لأَبِي حُصَيْنٍ : كَمْ تَعْبُدُ الْيَوْمَ مِنْ إِلَهٍ ؟ قَالَ : سَبْعَةً : سِتَّةٌ فِي الأَرْضِ ، وَوَاحِدٌ فِي السَّمَاءِ قَالَ : فَأَيُّهُمْ تَعُدُّ لِرَهْبَتِكَ وَلِرَغْبَتِكَ ؟ قَالَ : الَّذِي فِي السَّمَاءِ
Ma'ana: imran bin husain yace; annabi ya tambayi mahaifina husain, yace masa Allah nawa kake bautawa? Sai yace bakwai, guda shida suna kasa guda daya kuma yana sama. Sai annabi yace idan kashiga kunci ko kanason samun sauki wanne kake kira? Sai yace wanda yake sama.
(baihaqi 894)
Awani hadisin kuma akace:- -------------------------
Zan cigaba insha Allah.
AL'ARSHI
(Cigaba)
Awani hadisin kuma akace:-
حدثنا زكريا بن يحيى الساجي ثنا هدبة بن خالد ثنا حماد ابن سلمة عن عاصم عن زر عن ابن مسعود أنه قال : ما بين السماء الدنيا والتي تليها مسيرة خمس مئة عام ومابين كل سماء مسيرة خمس مائة عام وما بين السماء السابعة والكرسي مسيرة خمس مئة عام وما بين الكرسي والماء مسيرة خمس مئة عام والعرش على الماء والله عز و جل على العرش يعلم ما أنتم عليه
Ma'ana:- tsakanin saman duniya da wadda take bimata tafiyar shekara dari biyar ne, tsakanin kowace sama da wadda take bi mata tafiyar shekara dari biyar ne. tsakanin sama ta bakwai da kursiyyi tafiyar shekara dari biyar ne, tsakanin kursiyyi da ruwanda yake sama shima tafiyar shekara dari biyar ne, ita kuma al'arshi tana kan ruwan, shikuma Allah yanakan al'arshi.
(mu'ujamul kabir 8987)
Awani hadisin kuma akace:-
وعن العباس بن عبد المطلب - رضي الله عنه - قال: قال رسول الله - صلى الله عليه وسلم -: (هل تدرون كم بين السماء والأرض؟) قلنا: الله ورسوله أعلم قال: (بينهما مسيرة خمسمائة سنة، ومن كل سماء إلى سماء مسيرة خمسمائة سنة وكثف كل سماء خمسمائة سنة، وبين السماء السابعة والعرش بحر بين أسفله وأعلاه كما بين السماء والأرض، والله - سبحانه وتعالى - فوق ذلك، وليس يخفى عليه شيء من أعمال بني آدم)
Ma'ana: annabi sallallahu alaihi wasallam yace:- shin kunsan adadi nisanda yake tsakanin sama da kasa? Sai sahabbai sukace ai Alllah da manzonsane suka sani. Sai annabi yace:- tazararsu nisan tafiyar shekara dari biyar ce, sannnan daga kowace sama zuwa samanda take biye da ita shima nisan tafiyar shekara dari biyar ne, tsakanin samata bakwai da al'arshi kuma wani kogine, nisan dayake tsakanin saman kogin da kasan sa kamar nisan dayake tsakanin sama da kasa ne. shikuma Allah madaukaki yana saman haka(al'arshi) amma duk da haka ayyukan bani adam basa buya agareshi.
Toh tunda mun kawo ayoyi da hadisai dasuka nuna cewa Allah yana sama, yazu kuma zan juya bangaren manyan malamanmu nada domin ganin fatawowinsu gameda wannan aqidar.
Daga ibn Abbas
أخبرنا الحسن بن عثمان قال أخبرنا علي بن محمد بن الزبير قال ثنا إبراهيم بن أبي العنبس قال ثنا يعلي بن عبيد عن سفيان عن أبي هاشم عن مجاهد قال
قيل لابن عباس إن ناسا يقولون بالقدر
فقال يكذبون بالكتاب لئن أخذت بشعر أحدهم لا نضونه
إن الله عز و جل كان على عرشه قبل أن يخلق شيئا فخلق الخلق فكتب ما هو كائن إلى يوم القيامة فإنما يجري الناس على امر قد فرغ منه
Ma'ana; mujahid yacewa Abdullahi bn Abbas"mutane suna tayin maganganu akan qaddara
Sai ibn Abbas yace "hakika Allah mabuwayi yana al'arshinsa tun kafin ya halicci komai, sannan kuma ya halicci halittu sannan yarubuta duk abinda zai faru dasu har izuwa ranar qiyama, duk abinda kaga faru akan mutane toh dama abinda aka rubuta ne".
Acikin bayanin ibn Abbas zamuga inda yake tabbatarda aqidar cewa Allah yana sama.
Daga ibn Abbas din dai
أخبرنا أحمد بن محمد أخبرنا عبد الله بن محمد بن زياد قال ثنا ابن شيرويه قال ثنا إسحاق بن راهوية قال أخبرنا إبراهيم بن الحكم بن ابان عن ابيه
عن عكرمة في قوله ثم لأتينهم من بين أيديهم ومن خلفهم وعن ايمانهم وعن شمائلهم قال
قال ابن عباس لم يستطع أن يقول من فوقهم علم أن الله من فوقهم
Ma'ana: ikhrama yana tambayar ibn Abbas gameda ayarda shidan yayi rantsuwa yace zai biyowa dan adam ta damansa da hagunsa da gabansa da bayansa; sai ibn Abbas yace "baice zai biyo ta samansu ba saboda yasan Allah yana samansu".
Wannan ma dalili ne gameda cewa Allah yana sama.
Daga bashar bin umar
وأخبرنا أحمد أخبرنا عبد الله ثنا ابن شيرويه ثنا إسحاق أخبرنا بشر بن عمر قال
سمعت غير واحد من المفسرين يقولون الرحمن على العرش استوى قال على العرش استوى ارتفع
Ma'ana: bashar bin umar yace naji dayawa daga cikin masu fassara suna cewa gameda ayar alal arshistawa, ana nufin asamanta.
Daga ummu salamah
أخبرنا عبد الله بن محمد بن أحمد قال ثنا عبد الصمد ابن علي قال حدثني محمد بن عمر بن كبيشة أبو يحيى النهدي بالكوفة في جبانة سالم قال حدثنا أبو كنانة محمد بن أشرس الأنصاري قال ثنا أبو عمير الحنفي عن قرة بن خالد عن الحسن عن امه
عن أم سلمة في قوله الرحمن على العرش ا قالت الكيف غير معقول والاستواء غير مجهول
والاقرار به إيمان والحجود به كفرستوى
Ma'ana: ummu salamah tace: fadin yaya Allah ya daidaita akan al'arshi ba sanannen abu bane da hankali zai riska, sannan shikuma daidaito ba boyayyen abu bane, tabbatarda daidaiton nasa imani ne, kore daidaitar Allah akan al'arshinsa kafirci ne (inji ummu salamah ba inji awaisu haruna al'arabee ba).
Imamu malik bin Anas
ذكره علي بن الربيع التميمي المقري قال ثنا عبد الله ابن أبي داود قال ثنا سلمة بن شبيب قال ثنا مهدي بن جعفر
عن جعفر بن عبد الله قال
جاء رجل إلى مالك بن أنس فقال يا أبا عبد الله الرحمن على العرش استوى كيف استوى
فقال الكيف غير معقول والاستواء منه غير مجهول والإيمان به واجب والسؤال عنه بدعة
Ma'ana: wata rana wani mutum yazo wajen imamu malik, yace masa: Allah yace " الرحمن على العرش استوى " sai yace ya imamu shin yaya daidaiton yake?
Sai imamu malik yace, shidai sanin yaya ya daidaita ba sanannen abu bane, amma ai shi daidaito sanannen abu ne, sannan imani da daidaito wajibine, tambayar yaya Allah ya daidaita kuma bidi'ah ne.
Daga imam rabi'ah
اخبرنا عبد الله بن أحمد بن القاسم بن شينك النهاوندي قال ثنا أبو بكر أحمد بن محمود بن يحيى داود النهاوندي بنهاوند سنة ثنتي عشرة وثلثمائة قال ثنا أحمد بن محمد بن صدقة قال ثنا أحمد بن محمد بن يحيى بن سعيد القطان عن يحيى بن آدم عن ابن عيينة قال
سئل ربيعة عن قوله الرحمن على العرش استوى كيف استوى
قال الاستواء غير مجهول والكيف غير معقول ومن الله الرسالة وعلى الرسول البلاغ وعلينا التصديق
Ma'ana: antambayi rabi'ah gameda ayar istiwa'i. akace yaya istiwa'I yake?
Sai imam rabi'ah yace: shidai daidaito sanannen abu ne,sanin yaya ya daidaita ba abinda hankali zai dauka bane, aikin Allah kawai shine yayi aike, aikin manzo kuma shine ya isar da aikenda akayi masa, mukuma aikinmu shine mu gaskata abinda manzon yafada mana.
Daga ibnul arabee
اخبرنا محمد بن جعفر النحوي إجازة ثنا أبو عبد الله نقطوية قال حدثني أبو سليمان داود بن علي قال
كنا عند ابن الاعرابي فأتاه رجل فقال له
ما معنى قول الله عز و جل الرحمن على العرش استوى
فقال هو على عرشه كما أخبر عز و جل
فقال يا أبا عبد الله ليس هذا معناه إنما معناه استولى
قال اسكت ما انت وهذا لا يقال استولى على الشيء إلا أن يكون له مضاد فإذا غلب أحدهما قيل استولى
Ma'ana: wani yazo wajen ibnul arabee ya tambayesa gameda ayar istiwa'i. sai ibnul arabee yace ai Allah yana saman al'arshinsa kamar yadda yafada.
Sai mutumin yace aa ibnul arabee, ai ana nufin (استولى) ne, wato mamayewa.
Sai ibnul arabee yace "kai yimin shiru, kaikuwa wani irin mutum ne?, ana fadin istaula ne yayinda aka samu abubuwa kishiyoyin juna suke rikici akan wani abu, toh yayinda daya yayi galaba ya mamaye abin toh sai ace istaula".
Daga ibnul arabee din dai
أخبرنا أحمد بن محمد بن موسى بن القاسم حدثنا أبو بكر الأنباري قال ثنا أبو بكر محمد بن أحمد بن النضر وهو ابن بنت معاوية بن عمرو قال
كان أبو عبد الله بن الاعرابي جارنا وكان ليله أحسن ليل وذكر لنا أن ابن أبي داود سأله أتعرف في اللغة استوى بمعنى استولى فقال لا أعرف
Ma'ana: watarana ibnu abi dawud ya tambayi ibnul arabee yacemasa : ya ibnul arabee shin ayaren larabci kasan inda kalmar ' استوى ' take juyawa ta dauki ma'anar kalmar ' استولى '?
Sai ibnul arabee yace a'a ban sani ba.
Daga muqatil bin hayyan.
أخبرنا محمد بن الحسين بن يعقوب قال أخبرنا دعلج ابن أحمد قال ثنا أحمد بن علي الأبار قال ثنا محمد بن منصور الطوسي قال ثنا نوح بن ميمون قال ثنا بكير بن معروف
عن مقاتل بن حيان في قوله تعالى ما يكون من نجوى ثلثه إلا هو رابعهم ولا خمسة إلا هو سادسهم
قال هو على العرش ولن يخلو شيء من علمه
Ma'ana: muqatil yace gameda ayarda nakawo asama, sai yace Allah yana al'arshinsa amma ba abinda yaboyu ga iliminsa.
Daga imam at-taymiy
أخبرنا أحمد بن عبيد قال أخبرنا محمد بن الحسين قال أخبرنا أحمد بن أبي خيثمة قال حدثنا هارون بن معروف قال ثنا ضمرة عن صدقه قال
سمعت التيمي يقول لو سئلت أين الله تبارك وتعالى
قلت في السماء
فإن قال فأين عرشه قبل أن يخلق السماء
قلت على الماء
فإن قال لي أين كان عرشه قبل أن يخلق الماء
قلت لا أدري
Ma'ana: imam at-taymiy yace: da ace za'a tambayeni a ina Allah yake danace yana sama, idan akacemin a ina al'arshinsa take kafin yahalacci saman? Sai nace akan ruwa. Idan aka tambayeni a ina al'arshin take kafin ya halacci ruwan? Sai nace bansani ba.
Daga sufyanus-sauriy
أخبرنا أحمد بن عبيد قال أخبرنا محمد بن الحسين قال ثنا أحمد بن زهير قال ثنا يحيى بن معين قال ثنا علي بن الحسين ابن شقيق عن عبد الله الله بن موسى الضبي عن معدان قال
سألت سفيان الثوري عن قوله وهو معكم أينما كنتم
قال علمه
Ma'ana: ma'adan yace natambayi sufyanus-sauri gameda ayar da aka kawo asama, sai yace ai iliminsa ake nufi.
Daga Abdullahi bin nafi'i
أخبرنا محمد بن عبد الله بن الحجاج قال أخبرنا أحمد بن الحسين قال ثنا عبد الله بن أحمد قال ثنا أبي قال ثنا سريج بن النعمان قال
حدثني عبد الله بن نافع قال ملك الله في السماء وعلمه في كل مكان لا يخلو منه شيء
Ma'ana: yace mulkin Allah yana sama amma iliminsa yana ko ina,babu abinda yake boyuwa gareshi.
Imamu Ahmad bin Hambal
وروى يوسف بن موسى البغدادي أنه قيل لأبي عبد الله أحمد بن حنبل الله عز و جل فوق السماء السابعة على عرشه بائن من خلقه وقدرته وعلمه في كل مكان
Ma'ana: imamu Ahmad yace Allah yana saman samansa ta bakwai akan al'arshin sa, amma ya game bayinsa da iliminsa da qudurarsa wadanda suke ko ina.
Zan tsaya da kawo dalilai anan ba don sun kare ba sai domin shiga wani abin mai muhimmanci da ba wannan ba.
Idan baka manta ba nayi alkawarin zankawo dalilai na shari'ah dana hankali. Toh yanzu nakawo ba shari'ah yanzu kuma zan kawo dalili na hankali dazasu tabbatar mana da cewa Allah yana sama.
1)idan mutun zaiyi addu'ah ina yake daga hannunsa? Sama ko? Toh mai yasa yakeyin hakan?
2)Lokacinda Allah yayi isra'I da manzonsa ina yakaishi?
3)Lokacinda aka bawa annabi salloli hamsin ai yagamuda annabi musa sai yace masa yakoma arage masa domin al'ummarsa bazasu iya ba, da annabi ya tashi komawa ina yakoma? Sama ko kasa? Wajen wa?
4)Da akace kullum Allah yana saukowa da tsakar dare zuwa saman duniya daga ina yake saukowa? Ko ana saukowa daga kasa zuwa sama ne?
5)Idan kayi sujjada mai kake cewa?
6)Da sama da kasa inane yafi matsayi da martaba?
Wani zaice ai ba'a yiwa Allah wuri. Toh ai idan nace yana sama wuri daya nayi masa, kaikuwa dakace yana ko ina ai wurare dayawa kayi masa.
Wani kuma zaice ai mun siffanta Allah da bayinsa sabida mun ce ya daidaita akan al'arshinsa. Toh ai bamuce ga yadda ya daidaita din ba tunda bai gayamana na ba.
KAMMALAWA
Bayan dalilai da muka kawo da shari'ah dana hankali gameda wannan mas'alar muna godewa Allah madaukaki wanda ya daidaita akan al'arshinsa daya bamu dama da ikon yin wannan rubutun. Sannan ina kira ga yan uwana dalibai da muji tsoron Allah mu yarda da duk abinda mukaga yanada dalili bawai kawai wani malami ya bamu abinda babu dalili ba kuma murufe idamu mubishi ahaka.
Kaga wannan rubutun nawa wallahi har nagama bincikena akansa banci karo da wani nassi ba gada Allah ko manzonsa ko maganarwani sahabi ko tabi'I koma wani malaminda duniya ta yarda cewa malami ne ba daya nuna cewa Allah yana ko ina. inda ace nagani dana rubuta muku kodan bayarda hakkin ilimi.
Kamar kullum ina nan ina jiran tambaya, shawara ko karin bayani gameda wannan rubutun nawa.
Inaso yan uwana musulmi mu maida hankali wajen addu'ah ga yan uwanmu musulmi na yankin afrika ta tsakiya , maiduguri da sauran kasashen musulmi da ake zaluntarsu. Muna rokon Allah yabawa kasarmu lafiya da zaman lafiya ameen summa ameen.
Maimakon wasu maganganu na yabo ko makamancin haka da wsu sukeyi gameda mu; zanso ace addu'ah zakuyi akan Allah yabani ilimi mai amfani sannan yabani damar amfani da ilimin ta hanyar daya dace kuma yabani dama da fasahar isarwa da bayinsa sakon ta hanya mai kyau.
AWAISU HARUNA
AL'ARABEE
FAGGE
KHALIFANCIN SAYYADI ABUBAKAR R.A.
Gabatarwa
إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستهديه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا ومن سيئات أعمالنا من يهده الله فلا مضل له ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن لا إله إلا الله وحده لا شريك له ، وأشهد أن محمد عبده ورسوله : ( يَا أَيُّهَا النَّاسُ اتَّقُوا رَبَّكُمْ الذِي خَلقَكُمْ مِنْ نَفْسٍ وَاحِدَةٍ وَخَلقَ مِنْهَا زَوْجَها وَبَثَّ مِنْهُمَا رِجَالا كَثِيرًا وَنِسَاءً وَاتَّقُوا اللهَ الذِي تَتَساءَلُونَ بِهِ وَالأَرْحَامَ إِنَّ اللهَ كَانَ عَليْكُمْ رَقِيبًا ) ، أما بعد فإن خير الحديث كتاب الله وخير الهدي هدي محمد صلى الله عليه وسلم وشر الأمور محدثاتها وكل محدثة بدعة وكل بدعة ضلالة وكل ضلالة في النار .
Bayan haka; ina yiwa yan uwana musulmi sallama irin ta addinin musulunci Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.
Bayan haka, wannan rubutun nawa nayi shi ne domin amsa wata tambaya da wani bawan Allah yayi min kwanaki kadan dasuka wuce.
Yakamata nabashi amsa ta inda ya turo min tambayar, toh amma nafito da ita ne domin na fahimci cewa ina yawan samun iri-iren tambayar a comment din da akeyiwa rubututtuka na musamman wanda namusu taken 'falalar sahabbai'. Sai naga yadace tayi takaitaccen bayani akan tambayar sai ya zamanto koda wani yayi min irinta kawai zanyi masa ishara ne ga wannan rubutun. Ina fata Allah zaiyimin muwafaqa acikin rubutun wajen rubuta daidai da qudurce daidai acikin zuciyata, kuma ina fata wannan rubutun yazamanto hanyar shiriya ga mai tambayar.
SASHI NA FARKO
Tambayar da wanda ya turo ta.
Wanda ya rubuto tambayar shine DEEN EL-YUSUF ARRAFIDHY
Tambayar tasa itace: daga cikin maganganuka kace tuntuni isharori suka tabbata daga annabi SAW gameda nunin halifancin Abubakar a bayansa. Wadanne isharori ne suka tabbata????
SASHI NA BIYU
Amsar tambayarsa:
Gaskiyane abinda kafada na cewa nace isharori sun tabbata gameda halifancin sayyadi Abubakar abayan ma'aiki sallahu alaihi wasallam.
Abubuwa dayawa sun faru a zamani manzo SAW kuma har ya fadi wadansu abubuwa kuma yayi umarni da wasu abubuwan da suke nuna cewa bayan wafatinsa babu wanda ya dace halifance shi kamar sayyadi Abubakar radiyallahu ta'ala anhu. Ga kada daga ciki
أَخْبَرَنَا أَبُو عَبْدِ اللَّهِ الْحَافِظُ ، أَخْبَرَنَا أَبُو بَكْرِ بْنُ إِسْحَاقَ الْفَقِيهُ ، أَخْبَرَنَا إِسْمَاعِيلُ بْنُ قُتَيْبَةَ ، حَدَّثَنَا يَحْيَى بْنُ يَحْيَى ، أَخْبَرَنَا أَبُو مُعَاوِيَةَ ، عَنِ الأَعْمَشِ ، عَنْ إِبْرَاهِيمَ ، عَنِ الأَسْوَدِ ، عَنْ عَائِشَةَ ، قَالَتْ : لَمَّا ثَقُلَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم جَاءَ بِلالٌ يُؤْذِنُهُ بِالصَّلاةَ ، قَالَ : مُرُوا أَبَا بَكْرٍ فَلْيُصَلِّ بِالنَّاسِ فَذَكَرَ الْحَدِيثَ ، قَالَتْ : فَلَمَّا دَخَلَ فِي الصَّلاةِ وَجَدَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم مِنْ نَفْسِهِ خِفَّةً قَالَ : فَقَامَ يُهَادَى بَيْنَ رَجُلَيْنِ وَرِجْلاهُ تَخُطَّانِ فِي الأَرْضِ ، فَلَمَّا دَخَلَ الْمَسْجِدَ سَمِعَ أَبُوَ بَكْرٍ حِسَّهُ ذَهَبَ لِيَتَأَخَّرَ فَأَوْمَأَ إِلَيْهِ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم : قُمْ مَكَانَكَ فَجَاءَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم حَتَّى جَلَسَ عَنْ يَسَارِ أَبِي بَكْرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَتْ : فَكَانَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم يُصَلِّي بِالنَّاسِ جَالِسًا وَأَبُو بَكْرٍ قَائِمًا يَقْتَدِي أَبُو بَكْرٍ بِصَلاةِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم وَيَقْتَدِي النَّاسُ بِصَلاةِ أَبِي بَكْرٍ
Ma'ana: ankarbo hadisi daga nana A'isha R.A tace '' a lokacinda jikin annabi SAW ya nauyaya (lokacinda bashi da lafiya) sai Bilalu yazo yana sanar dashi cewa lokacin sallah yakarato, sai annabi SAW yace masa aje ace Abubakar yayiwa mutane sallah. Nana A'isha tace: A yayinda Abubakar yafara sallar sai annabi SAW yadan ji karfin jikinsa sai yasa wasu mutane guda biyu sukazo ya dafa kafadunsu yana dan taka kafafunsa yayinda ya shiga masallacin sai Abubakar yaji alamun shigowarsa, sai abubakar yayi nufin dawowa baya domin annabi ya wuce gaba yacigaba da sallah, sai annabi yayi masa nuni ga cewa ya tsaya a inda yake, sai annabi yazo ya zauna a hagun Abubakar. Sai annnabi yakasance yana yiwa mutane sallah a zaune, shikuma abubakar yana koyi da shi a tsaye, sukuma mutane suna koyi da abubakar''.
(sunanus-sugrah 515, sunanul kubra 3171, mu'ujamul awsad 5005, sunanu abi dawud 942, sunanu ibn majah 1232, sunanu tirmiziy 3672, sunanu daru qudniy, 5, sunanu nasa'I, 793, sahihu ibn khuzaimah 1616, sahihu bukhriy 633, sahihu muslim 967, musnad abi ya'ala 7524, musnad ahmad 13093,) (hadisun sahihun)
SHARHIN HADISIN
Sallah tana daga cikin manya manyan al'amuran addinin musulunci, falalar annabin rahama itace tasa dole shine zaiyiwa mabiyansa sallah a matsayin liman. A lokacin da bazai iya fitowa sallah ba sai yasa Abubakar yayiwa mutane sallah, kenan a lokacin babu wanda yakaishi matsayi acikin sahabbai, sahabbai masu dinbin yawan gaske suna halarce awajen cikinsu harda sayyadina Aliyu RA, inda ace Ali yafi Abubakar matsayi da shi annabi zai saka yayiwa mutane sallah ba Abubakar ba.
A wani hadisin kuma akace
حَدَّثَنَا عُبَيْدُ اللَّهِ بْنُ سَعِيدٍ حَدَّثَنَا يَزِيدُ بْنُ هَارُونَ أَخْبَرَنَا إِبْرَاهِيمُ بْنُ سَعْدٍ حَدَّثَنَا صَالِحُ بْنُ كَيْسَانَ عَنِ الزُّهْرِىِّ عَنْ عُرْوَةَ عَنْ عَائِشَةَ قَالَتْ قَالَ لِى رَسُولُ اللَّهِ -صلى الله عليه وسلم- فِى مَرَضِهِ « ادْعِى لِى أَبَا بَكْرٍ وَأَخَاكِ حَتَّى أَكْتُبَ كِتَابًا فَإِنِّى أَخَافُ أَنْ يَتَمَنَّى مُتَمَنٍّ وَيَقُولَ قَائِلٌ أَنَا أَوْلَى. وَيَأْبَى اللَّهُ وَالْمُؤْمِنُونَ إِلاَّ أَبَا بَكْرٍ ».
Ma'ana: an karbo hadisi daga ummuna A'isha Allah yakara yarda gareta, tace "Annabi SAW yace min (a lokacin rashin lafiyarsa) jeki kirawo min mahaifinki da dan uwanki, (kirawosu domin) inyi wani rubutu, domin ina tsoron kada wani maburaci yayi burin (abinda yadace ga Abubakar), ina tsoron kada wani yace shine yafi cancanta, Allah da muminai sunki kowa (yafara kasantuwa)sai Abubakar"
(sunanul kubra 16365, mu'ujamul awsad 4567, sunanu tirmiziy 3937, sunanud darimiy 82, sunanun nasa'I 7081, sha'abul iman 9130, sahihu muslim 6332, musnad ahmad 25133,) (rank: sahih)
Al'amarin wannan hadisin a bayyane yake basai mun tsaya mun batarda tawada ba, kawai zan cigaba da wani abin daban.
A wani hadisin kuma akace
عن إبراهيم بن سعد بن إبراهيم ، عن أبيه ، عن محمد بن جبير بن مطعم ، عن أبيه ، أن امرأة ، أتت رسول الله صلى الله عليه وسلم فسألته عن شيء فأمرها أن ترجع فقالت : يا رسول الله إن رجعت فلم أجدك ؟ كأنها تعني الموت قال : « فأت أبا بكر رضي الله عنه »
Ma'ana: wata mata tazo wajen manzon Allah sallallahu alaihi wasallam kuma ta tambayeshi wani abu sai annabi SAW yace mata taje ta dawo, sai matar tace "toh ya manzon Allah idan nadawo ban same ka ba fah???, kamar tana nufin in yarasu, sai annabi SAW yace in kin dawo baki sameni ba sai kije wajen Abubakar RA.
(musnad ahmad 2206, sunanu tirmiziy 3676, sahihu ibn hibban 6656, sahihu muslim 3660) (ranka: sahih)
SHARHIN HADISI
Koda a shugabanninmu na yanzu ai idan aka gaiyace su waje bazasu samu damar zuwa ba ai mataimakansu suke turawa. Idan bako sukayi wanda bazasu samu damar ganinsa ba ai mataikin ake sakawa ya gana da bakin.
A lokacinda matar tazo wajen annabi SAW bai samu damar amsa mata abinda tazo dashi ba saboda wani dalili da ba'a ambata ba a ruwayar hadisin, mutanen da masu cikakken imani ne da kuma hankali, tasan zata iya dawowa a lokacin bayanan, sai ta tambaye shi idan tazo bayanan wa zata nema?? Sai annabi sallallahu alaihi wasalam yace mata idan tazo bayanan toh tanemi abubakar, domin Annabi yana da masaniyar babu wanda ya dace da halifanci a bayansa sai shi sayyadi Abubakar din. Inda ace akwai wanda yafi Abubakar cancanta da al'amarin toh da shi Annabi zai ce ba Abubakar ba, domin hakan shine adalci, dama ai adalci shine ajiye komai a inda ya dace, shikuwa sanya abu a inda ba muhallinsa ba zalunci ne, duk mutum mai hankali kuwa bazai taba tunanin jingina zalunci ga shugaban halittun duk duniya da lahira ba. Allah yasa mudace.
A wani hadisin akace
عن عبد الملك بن عمير ، عن ربعي بن خراش ، عن حذيفة قال : قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : « اقتدوا باللذين من بعدي : أبي بكر وعمر »
Ma'ana: an karbo hadisi daga wanda yafi kowa sanin munafukai wato huzaifatul yamaniy, yace Annabi SAW yace " kuyi koyi da wadanda zasu biyo bayana, Abubakar da Umar"
حدثني عبد الله بن محمد حدثنا أبو عامر حدثنا فليح قال حدثني سالم أبو النضر عن بسر بن سعيد عن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه قال
: خطب رسول الله صلى الله عليه و سلم الناس وقال ( إن الله خير عبدا بين الدنيا وبين ما عنده فاختار ذلك العبد ما عند الله ) . قال فبكى أبو بكر فعجبنا لبكائه أن يخبر رسول الله صلى الله عليه و سلم عن عبد خير فكان رسول الله صلى الله عليه و سلم هو المخير وكان أبو بكر أعلمنا فقال رسول الله صلى الله عليه و سلم ( إن من أمن الناس علي في صحبته وماله أبا بكر ولو كنت متخذا خليلا غير ربي لاتخذت أبا بكر ولكن أخوة الإسلام ومودته لا يبقين في المسجد باب إلا سد إلا باب أبي بكر )
Ma'ana:- manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yayiwa mutane khuduba, aciki sai yake cewa "hakika Allah yabawa bawansa zabi na abinda yake na rayuwar duniya da kuma wanda yake wajensa (shi Allah), sai bawan ya zabi abinda yake wajen Allah", sai sayyadina abubakar yafashe da kuka har sahabbai suka dinga mamakin abinya yasaka shi kukan, sai yake fada musu cewa ai annabi shine bawan da aka bawa zabin. Sai Annabi SAW yacigaba da cewa "hakika Abubakar yana daga cikin wadanda nafi amintuwa dasu awajen dukiyarsu da kuma abokantaka ta dasu. Da ace bayan ubangiji na zan iya rikar wani a matsayin badadi na to da Abubakar zan rika, amma yanzu saide so da kauna na musulunci kawai. Daga yau ku toshe duk kofofinda suke kawo ku masallaci amma banda kofar Abubakar."
A wancan lokacinda abubuwa basu fadada ba masallaci shine the only islamic center, anan ake taro, meeting, shari'ah, karatu da sauran abubuwanda suka shafi addinin musulunci, amma banda haddi, shi ba'a yinsa acikin masallaci. Tunda kuwa hakane, toh yakamata ace gidan shugaban al'ummar musulmi yana kusa kusa da massallaci domin sauwakewa al'ummarsa saduwa izuwa gareshi.
Hakanne yasa gidan manzon rahama ya kasance mafi kusa da masallaci, sannan hasalima yasa aka fasa masa kofa daga gidanshi zuwa masallaci, ta yarda yana bude kofar gada cikin gidansa zai shiga masallaci direct. Shine ma har hadisi yazo cewa a lokacinda yake yin ibadar ittiqafi yakan zuro kansa ta window domin ummuna A'isha RA ta taje masa ta shafa masa mai a kan nasa.
Toh suma sahabbai mutane ne masu son addini ne, suma sai suka fasa nasu kofofin daga gidajensu zuwa masallaci.
Toh a karshen wannan khudubar ta annabi sai yayi umarnin kowa ya toshe kofar daya fasa wadda zata dinga kawo shi masallaci, amma banda Abubakar shi ba sai ya toshe tashi ba.
Kuma hakan ishara ne nacewa bayan wafatin Annabin rahama SAW shi sayyadi abubakar shine zai zama shugaban al'ummar musulmi, kaga kuwa zaifi dacewa yakasance yana kusa-kusa da masallaci.
YANZU KUMA BARI MU JUYA BANGAREN AYOYI
Allah yace
وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَالرَّسُولَ فَأُولَئِكَ مَعَ الَّذِينَ أَنْعَمَ اللَّهُ عَلَيْهِمْ مِنَ النَّبِيِّينَ وَالصِّدِّيقِينَ وَالشُّهَدَاءِ وَالصَّالِحِينَ
Ma'ana:- duk wanda yayiwa Allah da manzonsa biyayya, toh hakika yana tareda wadanda Allah yayiwa ni'ima daga cikin manzanninsa, da masu gaskiya, da shahidai da kuma salihan bayi.
SHARHI
Idan ka kakalli jerin ayar, zaka ga duk duniya babu wanda yafi kowa matsayi sai wanda yakasance annabi, daga shi kuwa sai siddiki sannan shahidi sannan salihan bayi.
Toh kuwa kasan ai annabi Muhammad SAW yafi kowa, dama kuma ai kasan babu annabi bayan shi, toh kenan sai siddiqi ko? Toh waye siddiqin wannan al'umar??? Amsa: abubakar siddiq. Hadisi kuwa yazo hada sayyadi ali cewa Allah ne ya sakawa abubakar sunan siddiq annabi ko sahabbai ba.
Ga hadisin
قَالَ عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ: « إِنَّ الله أَنْزَلَ اسْمَ أَبِي بَكْرٍ مِنَ السَّمَاءِ: الصِّدِّيق »؛ وَكَانَ يَحْلِفُ عَلَى ذَلِكَ
Ma'ana: Aliyu bin Abi Dalib yace: Allah ne ya saukar da sunan Abubakar: SIDDIQ daga sama. Sayyadi Ali har yakasance yana rantsuwa akan hakan.
(1) « معرفة الصَّحَابَة » لأبي نُعيمٍ (1/150).
(2) أَخْرَجَهُ الطَّبَرَانيُّ فِي « الْمعجم الْكَبِير » (1/55)، وَذكره الْحَافِظُ ابْن حَجَرٍ فِي « الْفَتْح » (7/11) وَقَالََ: « رِجَالهُ ثِقَاتٌ »
Kaga kenan wannan ayar ma zata zama dalili akan halifancinsa a karin fari.
Awata ayar kuma Allah yace
قل للمخلفين من الأعراب ستدعون إلى قوم أولي بأس شديد تقاتلونهم أو يسلمون فإن تطيعوا يؤتكم الله أجرا حسنا وإن تتولوا كما توليتم من قبل يعذبكم عذابا أليما
Ma'ana: (ya kai manzon Allah) kafadawa wadanda sukaki zuwa yaki(n hudaibiyyah) cewa da sannu za'a kiraku izuwa karawa dawasu mutane masu tsananin karfi sai ku yakesu kokuma su musulunta. Idan kukayiwa Allah da manzonsa biyayya wajen zuwa yakin toh kuna da lada mai yawa, amma idan kukaki kuma kuka juya kamar yadda kukayi abaya toh Allah zai azabtar daku azaba mai raddadi.
SHARHI
Da akace Wadanda suka ki zuwa yaki, yakinda ake nufi shine yakin hudaibiyyah, sukuma mutane masu karfinda akace za'ayi kira a yakesu sune ahlu yamama da juhainawa da muzainawa, toh wanene ya yakesu??? Sayyadina Abubakar ne ya yake su. Kaga kenan wannan ayar itama dalili ce mai karfi.
SASHI NA UKU
Warware wasu yan shubuhohi kokuma tambayoyinda mai musu zai iya dogaro dasu.
Yakamata tunda mun sansu mufara warwaresu tun farko don gudun jeka ka dawo.
Ai akwai masu ganin cewa sayyadi Ali shine ya dace yafara halifanci kafin Abubakar da Umar da Usman.
Kuma suna kafa hujja da wasu hadisai kamar haka.
Na farko
حَدَّثَنَا الْحُسَيْنُ بن إِسْحَاقَ التُّسْتَرِيُّ ، حَدَّثَنَا أَبُو الرَّبِيعِ الزَّهْرَانِيُّ ، حَدَّثَنَا حَمَّادُ بن زَيْدٍ ، حَدَّثَنَا أَبُو هَارُونَ الْعَبْدِيُّ ، عَنْ رَجُلٍ ، عَنْ زَيْدِ بن أَرْقَمَ ، أَنّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ، قَالَ لِعَلِيٍّ يَوْمَ غَدِيرِ خُمٍّ : اللَّهُمَّ مَنْ كُنْتُ مَوْلاهُ فَعَلِيٌّ مَوْلاهُ ، اللَّهُمَّ وَالِ مَنْ وَالاهُ وَعَادِ مَنْ عَادَاهُ .
Ma'ana:- Annabi SAW yafadawa sayyadi Aliyu a ranar GADIR KUM yace "duk wanda nakasance masoyinsa toh Aliyu ma masoyinshine, ya Allah kaso wanda yaso shi (Ali), ya Allah kaki wanda yaki shi".
(hadisi ne sahihi)
Su kuma yan shi'ah sai suke fassara hadisin a 'duk wanda nake shugabansa toh Aliyu ma shugabansa ne Allah kaso wanda yaso shi kuma kaki wanda yaki shi.'
Amma ko kadan ba haka fassarar take ba. wadda muka kawo abaya itace ingantacciyar fassarar hadisin
Amma bari mudanyi karin bayani kadan akan abinda hadisin ya kunsa.
Farko dai ita kalmar (مولى) tana kunsar abubuwa uku
Na farko: masoyi
Na biyu: mataimaki
Na uku: shugaba.
Toh acikin wadannan ma'anonin wacce ake nufi a hadisin????
Bari nayi adalci, bazan fadi nawa ra'ayin ba, zan dauki kowacce ma'ana sai nayi kokarin kareta da hujjojinda zasu karfafeta.
NA faRKO
Masoyi.
Kenan ma'anar hadisin shine, duk wanda ni masoyinshi ne toh Aliyu ma masoyinshi ne.
Menene zai goyi bayan wannan hujjar???
Amsa: ai dama Annabi yafada cewa
حدثنا عبد الله بن محمد ، ثنا أحمد بن عمران الأخنس ثنا | ابن فضيل ثنا أبو نصر عبد الله بن عبد الرحمن الأنصاري . عن مساور | الحميري ، عن أمه عن أم سلمة قالت : سمعت رسول الله صلى الله عليه | وسلم يقول لعلي في بيتي ' لا يحبك إلا مؤمن ولا يبغضك إلا منافق ' .
Ma'ana: ummusalama tace naji annabi SAW yana fadin wata magana akan sayyadi Aliy, yana cewa "babu mai son Ali sai mai imani kuma babu mai kin Aliyu sai munafiki"
Toh munafiki yana son Annabi ne? ai masu imani ne kawai suke son annabi, toh haka shima Aliyu ai munafukai basa sonsa, masu imani ne kawai suke son Aliyu.
Dama kuma ai Allah yace
والمؤمنين والمؤمنات بعضهم أولياء بعض
Ma'ana: muminai maza da muminai mata sashinsu masoya shashi ne.
Kaga kenan abinda zamu fahimta anan shine Annabi ba shugabanci yake nufin Aliyu dashi ba. yana nufin soyayya ne.
NA BIYU
Mataimaki
Allah yace
ذلك بأن الله مولى الذين آمنوا وأن الكافرين لا مولى لهم
Ma'ana: (hakan ya faru ne) saboda Allah shine mataimakin masu imani, sukuma kafirai basuda mataimaki.
Idan kace zaka fassara ayar da soyayya ana to zaka samu matsala, domin ai suma kafirai suna da masoya.
Awata ayar Allah yace
فإن الله هو مولاه وجبريل وصالح المؤمنين
Ma'ana" (idan kukace zaku tauye hakkinsa tofa) Allah shine mataimakinsa, haka jibrilu kuma hakama salihan bayi.
Awata ayar kuma Allah yace
ومن يتولى الله ورسوله والذين آمنوا فإن حزب الله هم الغالبون ) .
Ma'ana: duk wanda ya taimaki addinin Allah da manzonsa (wajen fita yaki) toh hakika rundunar Allah itace zatayi galaba (a filin yakin)
Wannan ayar tana daidai da ayarda Allah yace
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنْ تَنْصُرُوا اللَّهَ يَنْصُرْكُمْ وَيُثَبِّتْ أَقْدَامَكُمْ
Ma'ana: yaku wadanda sukayi imani, idan kuka taimaki addinin Allah toh shima zai taimakeku sannan zai tattabatarda diga-diganku(a filin yaki).
Wannan itace ma'ana ta biyu da kalmar take dauka, kuma itama wannan zata iya shiga karkashin fadin Annabi dayayiwa Aliyu RA.
NA UKU
Shugaba
Idan kace Annabi SAW yana nufin cewa duk wanda yake shugabansa toh Aliyu ma shugabansa ne, toh wannan bama sai ka bukaci aya ko hadisi ba kafinka rushe maganar, da karashen hadisin ma kawai zaka iya rushewa.
Idan kace haka fassarar take nufi toh zaka samu matsala a karshen hadisin, domin Annabi SAW cewa yayi
اللَّهُمَّ وَالِ مَنْ وَالاهُ وَعَادِ مَنْ عَادَاهُ
Kaga kenan fassararka zata kasance : Allah ka shugabantarda wanda ya shugabantar da Aliyu, domin ai de duk kalmar maula dince, kaga kenan indai shugabanci ake nufi a hadisin toh duk wanda ya yarda da shugabancin Aliyu toh shima yazama shugaba. Kuma duk duniyar masu hankali sun san hakan bazai yiwu ba.
Toh kaga kenan hadisin zai dauki ma'ana ta farko da da biyu amma banda ta uku.
A lokacinda Annabi SAW zai tafi yakin tabuka, sai ya kirawo sayyadi Ali yace ya halifance shi a madina kafin ya dawo, saboda dama ai ba'a kwasar jiki a tafi yaki gaba daya kamar yadda aya ta hana. Toh sai sayyadi Ali yace ya ma'aikin Allah baka ganin mutane zasuce bakason fita tare dani ne?? sai Annabi SAW yace masa shin bakaso kazamanto min kamar yanda Haruna ya zamanto ga Musa??? Saide kawai babu annabi bayana.
Wani zaice to ai tunda aka halifantar dashi toh ana nuna cewa shine halifa kenan. Amma samsam ba haka lamarin yakeba,
An halifantar dashi ne domin a lokacin duk wadanda suka rage basu je yaki ba babu wanda yakai Aliyun falala saide Usmanu.
Amma Abubakar yafita, Umar yafita shikuma Usman a lokacin yana jinyar yar gidan Annabi SAW ne, kaga kuwa bashi da nutsuwarda zai iya kulawa da al'umma kamar yadda wani zaiyi. Toh kuma dama sune suka fishi matsayi, tunda kuwa basa nan ai dole shine halifan lokacin.
Akwai wadansu shubuhohin amma dai wadannan sune sukafi shahara kuma sukafi rikitarda wadanda basa karatu. Amma in ana karatu duk abu ne mai sauki.
KAMMALAWA
Da dan wannan rubutn da kuka gani zan takaita wannan amsar. Ina fata wannan rubutun zai zama sanadiyar shiriya ga wanda yayi tambaya daa shi da yan uwansa.
Ina fatan Allah yabamu ladan abinda nayi daidai a rubutun. Shikuma kuskuren na fata Allah ya yafe min.
Allah yasa mudace amen.